عَنْ حُمْرَانَ مَوْلَى عُثْمَانَ بْنِ عَفَّانَ رضي الله عنه:
أَنَّهُ رَأَى عُثْمَانَ بْنَ عَفَّانَ دَعَا بِوَضُوءٍ، فَأَفْرَغَ عَلَى يَدَيْهِ مِنْ إِنَائِهِ، فَغَسَلَهُمَا ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَمِينَهُ فِي الْوَضُوءِ، ثُمَّ تَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ وَاسْتَنْثَرَ، ثُمَّ غَسَلَ وَجْهَهُ ثَلَاثًا، وَيَدَيْهِ إِلَى الْمِرْفَقَيْنِ ثَلَاثًا، ثُمَّ مَسَحَ بِرَأْسِهِ، ثُمَّ غَسَلَ كُلَّ رِجْلٍ ثَلَاثًا، ثُمَّ قَالَ: رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَتَوَضَّأُ نَحْوَ وُضُوئِي هَذَا، وَقَالَ: «مَنْ تَوَضَّأَ نَحْوَ وُضُوئِي هَذَا ثُمَّ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ لَا يُحَدِّثُ فِيهِمَا نَفْسَهُ غَفَرَ اللهُ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 164]
المزيــد ...
Daga Humran bararran bawa na Usman Dan Affan cewa ya ga Usman Dan Affan ya nemi da akawo masa ruwan alwala, sai ya karkato da kwaryar (butar Alwala), sai ya wankesu sau uku, sannan ya shigar da (hannunsa na) dama a ruwan alwalar, sannan ya kuskure baki ya shaƙa ruwa ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, da hannayensa zuwa gwiwar hannaye sau uku, sannan ya shafi kansa, sannan ya wanke kowacce ƙafa sau uku, sannan ya ce: Na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya yi alwala irin wannan alwalar tawa, sai ya ce: "Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu bai zantar da ransa a cikinsu ba, to, Allah Zai gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 164]
Sayyidina Usman - Allah Ya yarda da shi - ya karantar da siffar alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a aikace; don ya zama mafi fitowa ɓaro-ɓaro, sai ya nemi ruwa a ƙwarya, sai ya zuba a hannayensa sau uku, bayan haka ya shigar da hannunsa na dama a cikin ƙwaryar, sai ya ɗebo ruwa daga cikinta sai ya kurkura shi a bakinsa, sannan ya fitar da shi, sannan ya shaki ruwan da numfashinsa zuwa cikin hancinsa, sannan ya fitar da shi ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa tare da gwiwar hannaye sau uku, sannan ya shuɗar da hannunsa a kan kansa suna masu damshi da ruwa sau ɗaya, sannan ya wanke ƙafafuwansa tare da idon sawu sau uku.
Lokacin da ya gama - Allah Ya yarda da shi - sai ya ba su labarin cewa shi ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi alwala irin wannan alwalar, kuma [Annabi] - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi musu albishir da cewa wanda ya yi irin wannan alwalar, ya yi sallah raka'a biyu, yana mai khushu'i yana mai halarto da zuciyarsa a gaban Ubangijinsa - mai girma da ɗaukaka - a cikinsu, to, Allah Zai yi masa sakayya a kan wannan alwalar cikakkiya da wannan sallar tsarkakiyya da gafarta abin da ya gabata daga zunubansa.