عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إذا توضَّأ أحدُكُم فَليَجعَل في أنفِه ماءً، ثم ليَنتَنْثِر، ومن اسْتَجمَر فَليُوتِر، وإذا اسْتَيقَظَ أَحَدُكُم من نومِه فَليَغسِل يَدَيه قبل أن يُدْخِلهُما في الإِنَاء ثلاثًا، فإِنَّ أَحدَكُم لا يَدرِي أين بَاتَت يده». وفي رواية: «فَليَستَنشِق بِمِنْخَرَيه من الماء». وفي لفظ: «من توضَّأ فَليَسْتَنشِق».
[صحيح] - [الرواية الأولى: متفق عليها. الرواية الثانية: رواها مسلم. الرواية الثالثة: متفق عليها، ولفظ مسلم: (فليستنثر)، بدل: (فليستنشق)]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi : " Idan dayanku zai yi alwala sai ya sanya ruwa a hancinsa, sannan ya fato, wanda zai yi tsarki sai yi shi mara, IDan dayanku ya farka daga bacci to ya wanke hannayensa kafin shigar da su cikin abin alwala, domin bai san a inda hannunsa ya kwana ba
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Wannan hadisin ya kunshi sakin layi uku,kuma ko wane sakin layi yana dauke da hukuncinsa da ban.Na farko: An ambaci cewa mai alwalla zai shaka ruwa a hancinsa,ya kuma fyace shi, saboda hanci wani bangare ne na fuska,wacce aka yi umarni da a wanke ta.hadisai da yawa sun yi nuni akan shar'anta wanke fuska;don kuwa yana daga tsaftar da shari'a ta nemi ayi. Na biyu: wanda zai yi tsarkin hoge,to ana so yayi shi mara,mafi karanci sau uku,mafi yawansa kuma,a yi shi gwargwadon yadda tsarki zai tabbata. Na uku: wanda ya farka daga bacci bazai shigar da hannunsa cikin abin alwala,har sai ya wanke shi sau uku;saboda mafi yawanci baccin dare kan tsawaita,tana yiwuwa hannunsa ya tattaba ko ina a jikinsa har kazanta wanda ba lallai yasan hakan ba,sai aka umarce shi da wanke su don tsafta.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin