عن أنس بن مالك رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم كان إذا دخل الخَلاء قال: ((اللهم إني أَعُوذ بك من الخُبُثِ والخَبَائِث)).
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Anas dDan Malik - Allah ya yarda da shi -Annabi Mai tsira da aminci ya kasance in zai shiga bandaki yana cewa: [Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga shaidanu maza da shaidanu matan
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Anas Dan Malik wanda Allah ya daukake shi da yiwa Annabi tsira da amincin Allah hidima, yana ambata mana ladabin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayin biyan bukata, don kuwa saboda yawan kusancinsa da Ubangijinsa ba ya barin ambaton sa a kowane hali, Manzon Allah in zai shiga bandaki sai ya nemi Tsarin Allah ya kuma koma zuwa gare shi wajen neman ya kare shi daga sharrin guri mai najasa, kuma ya kare shi daga shaidanu mata,sune wadanda ke kokarin yiwa musulmi bace cikin lamarin addininsa da bautarsa

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Swahili
Manufofin Fassarorin