+ -

عَنْ أَبِي أَيُّوبَ الأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِذَا أَتَيْتُمُ الغَائِطَ فَلاَ تَسْتَقْبِلُوا القِبْلَةَ، وَلاَ تَسْتَدْبِرُوهَا وَلَكِنْ شَرِّقُوا أَوْ غَرِّبُوا» قَالَ أَبُو أَيُّوبَ: فَقَدِمْنَا الشَّأْمَ فَوَجَدْنَا مَرَاحِيضَ بُنِيَتْ قِبَلَ القِبْلَةِ فَنَنْحَرِفُ، وَنَسْتَغْفِرُ اللَّهَ تَعَالَى.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 394]
المزيــد ...

Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma" Abu Ayyub ya ce: Sai muka je Sham sai muka samu banɗakuna an gina su ɓangaren alƙibla sai mu juya, muka nemi gafarar Allah - Maɗaukakin sarki -".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 394]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi nufin biyan buƙatarsa na fitsarine ko bayan gida ya fuskanci alƙibla wajen Ka'aba, kuma kada ya juya mata baya, ya sanyata a bayansa; kai ya wajaba akansa ne ya juya ɓangaren gabas ko yamma idan alƙiblarsa kamar alƙiblar mutanen Madina ce. Sannan Abu Ayyub - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su lokacin da suka je Sham sun samu banɗakunan da aka tanada dan biyan buƙata a cikinsu an gina su suna fuskantar Ka'aba, sun kasance suna juyawa alƙibla baya da jikkunasu, tare da hakan suna neman gafarar Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hikima a hakan shi ne girmama Ka'aba maɗaukakiya da ganin alfarmarta.
  2. Neman gafara bayan fitowa daga gurin biyan buƙata.
  3. Kyakkyawan koyarwar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi lokacin da ya ambaci wanda aka hana sai ya shiryar zuwa ga wanda ya halatta.