+ -

عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه قَالَ:
كُنْتُ رَجُلًا مَذَّاءً وَكُنْتُ أَسْتَحْيِي أَنْ أَسْأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِمَكَانِ ابْنَتِهِ فَأَمَرْتُ الْمِقْدَادَ بْنَ الْأَسْوَدِ فَسَأَلَهُ فَقَالَ: «يَغْسِلُ ذَكَرَهُ وَيَتَوَضَّأُ». وَلِلبُخَاريِّ: فَقَالَ: «تَوَضَّأْ وَاغْسِلْ ذَكَرَكَ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 303]
المزيــد ...

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kasance mutum ne mai yawan maziyyi, na kasance ina jin kunyar tambayar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda matsayin 'yarsa sai na umarci Mikdad Dan Aswad sai ya tambaye shi sai ya ce: "Ya wanke gabansa ya yi alwala". Ga Bukhari: Sai ya ce: "Ka yi alwala ka wanke gabanka".

Ingantacce ne - Buhari ne ya rawaito shi

Bayani

Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa ya kasance da yawan maziyyi yana fita daga gare shi - shi wani ruwa ne fari siriri mai zuba yana fita daga gaba a yayin sha'awa ko kafin jima'ai -. Bai san me zai aikata ba idan ya fita ba, sai ya ji kunyar ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi mijin Fadimatu ne 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya bukaci Mikdad Dan Aswad ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hakan, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa da ya wanke gabansa sannan ya yi alwala.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الغوجاراتية القيرقيزية النيبالية اليوروبا الدرية الصومالية الكينياروندا التشيكية المالاجاشية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar Aliu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -, yadda kunya ba ta hana shi barin tambayaba ta hanyar (wani).
  2. Halaccin wakilci a neman fatawa.
  3. Halaccin mutum ya baiwa wani labarin abinda yake jin kunyar shi domin wata maslaha.
  4. Najasar maziyyi, da wajabcin wanke shi daga jiki da tufafi.
  5. Fitar maziyyi yana daga abubuwa masu bata alwala.
  6. Wajabcin wanke gaba da maraina dan zuwansa a wani hadisin daban.