عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: «جاء أعرابِيُّ، فبَالَ في طَائِفَة المَسجد، فَزَجَرَه النَّاسُ، فَنَهَاهُمُ النبِيُّ صلى الله عليه وسلم فَلمَّا قَضَى بَولَه أَمر النبي صلى الله عليه وسلم بِذَنُوب من ماء، فَأُهرِيقَ عليه».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- an daga hadisin zuwa ga Annabi: Wani balaraben kauye ya zo ya yi fitsari a wani bangare na masallaci,sai mutane suka kyare shi, sai Annabi ya hana su -tsira da aminci su tabbata a gare shi- bayan ya gama fitsarin sai Annabi tsira da amaincin Allah ya yi umarni da a zo da cikakken guga na ruwa, sai aka kwara akai
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Yana daga al'adar larabawan kauye, kausasawa da wauta, saboda nisansu da abin da Allah ya saukar ga Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.Wata rana Annabi tsira da amincin Allah ya kasance tare da sahabbansa a cikin masallacin Annabi, sai wani balaraben kauye ya zo ya yi fitsari a wani bangaren masallacin Annabi, tsammaninsa massallaci kamar fikli ne, sai abin ya ba sahabbai mamaki ba don komai ba sabo da girman alfarmar masallacin, sai suka tsawatar masa lokacin da yake fitsarin. sai dai Annabi maabocin kyawawan dabi'u, wanda aka aiko da bushara da sauki ya hana su, sabio da saninsa da halayen larabawan kauye, kumadon kar ya bata gurare masu yawa a cikin masallacin, kuma don kada ya cutu idan aka yanke masa fitsarin, kuma yin hakan zai sa yafi karbar nasihar da koyarwar Manzo, don haka ya umarce su da su tsarkake gurin ta hanyar kwara ruwa cikin guga a wajen

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin