+ -

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ رضي الله عنهما أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِذَا دَخَلَ الرَّجُلُ بَيْتَهُ، فَذَكَرَ اللهَ عِنْدَ دُخُولِهِ وَعِنْدَ طَعَامِهِ، قَالَ الشَّيْطَانُ: لَا مَبِيتَ لَكُمْ، وَلَا عَشَاءَ، وَإِذَا دَخَلَ، فَلَمْ يَذْكُرِ اللهَ عِنْدَ دُخُولِهِ، قَالَ الشَّيْطَانُ: أَدْرَكْتُمُ الْمَبِيتَ، وَإِذَا لَمْ يَذْكُرِ اللهَ عِنْدَ طَعَامِهِ، قَالَ: أَدْرَكْتُمُ الْمَبِيتَ وَالْعَشَاءَ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2018]
المزيــد ...

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2018]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ambatan Allah a yayin shiga gida da kafin cin abinci, kuma cewa shi idan ya ambaci Allah da fadinsa: (Da sunan Allah) a lokacin shigarsa da kuma lokacin fara abincinsa, Shaidan zai cewa mataimakansa: Baku da rabo na makwanci ko abincin dare a wannan gidan da mai shi ya kare kansa daga ku da ambatan Allah - Madaukakin sarki -. Amma idan zai shiga gidansa bai ambaci Allah a lokacin shigarsa ba ko lokacin cin abincinsa, sai Shaidan ya sanar da mataimaknsa cewa sun sami makwanci, da abincin dare a wannan gidan.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so ambatan Allah a lokacin shiga gida da lokacin cin abinci, domin Shaidan yana kwana a cikin gidaje, yana ci daga abincin mutanen gidan idan ba su ambaci sunan Allah - Madaukakin sarki ba -.
  2. Shaidan yana lura da Dan Adam a cikin aikinsa da jujjuyawarsa acikin al'amauransa gaba dayansu, idan ya rafkana daga zikiri zai samu abin nufinsa daga gare shi .
  3. Zikiri yana kore Shaidan.
  4. Kowanne Shaidan yana da mabiya da masoya suna albishir da maganarsa kuma suna bin umarninsa.