kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

"Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa*, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: @ Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona*, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".
عربي Turanci urdu
"Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci*, idan ya farka sai ya ambaci Allah, sai kulli ɗaya ya warware, idan ya yi alwala sai ƙulli ɗaya ya warware, idan ya yi sallah sai ƙulli (ɗaya) ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai, inba haka ba sai ya wayi gari mai mummunar rai mai yawan kasala".
عربي Turanci urdu
"Misalin wanda yake ambatan Ubangijinsa da wanda ba ya ambatan Ubangijinsa, kamar rayayye ne da matacce"*, lafazin Muslim kuma: "Misalin gidan da ake ambatan Allah a cikinsa, da gidan da ba'a ambatan Allah a cikinsa, kamar rayayye ne da matacce".
عربي Turanci urdu
"Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".
عربي Turanci urdu
: :
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci Sinhalese
Mun kasance a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: @«Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?»* Sai wani mai tambaya daga mazauna wajen ya tambaye shi: Ta yaya ɗayammu zai samu kyakykyawan aiki dubu? Ya ce: «Ya yi tasbihi sau ɗari, sai a rubuta masa kyakykyawa dubu, ko kuma a sarayar masa da kura-kurai dubu».
عربي Turanci urdu
Lallai shaixan ya ce: Na rantse da Girmanka Allah, ba zan gushe ba ina vatar da Bayinka, matuqar dai rayukansu suna jikinsu, Ubangiji ya ce: Na rantse da Girmana da Xaukaka ta ba zan gushe ba ina gafarta musu matuqar sun nemi gafara ta
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya ce: Ina neman gafarar Allah, wanda babu wani abin bautawa face Shi wanda yake rayayye kuma mai rai kuma ya tuba zuwa gare Shi, an gafarta masa zunubansa, koda kuwa ya tsere daga cikin rarrafe
عربي Turanci urdu
«Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna».
عربي Turanci urdu
«(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa*: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».
عربي Turanci Indonisiyanci