عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«يَعْقِدُ الشَّيْطَانُ عَلَى قَافِيَةِ رَأْسِ أَحَدِكُمْ إِذَا هُوَ نَامَ ثَلاَثَ عُقَدٍ يَضْرِبُ كُلَّ عُقْدَةٍ عَلَيْكَ لَيْلٌ طَوِيلٌ، فَارْقُدْ، فَإِنِ اسْتَيْقَظَ فَذَكَرَ اللَّهَ، انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَإِنْ تَوَضَّأَ انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَإِنْ صَلَّى انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَأَصْبَحَ نَشِيطًا طَيِّبَ النَّفْسِ، وَإِلَّا أَصْبَحَ خَبِيثَ النَّفْسِ كَسْلاَنَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1142]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci, idan ya farka sai ya ambaci Allah, sai kulli ɗaya ya warware, idan ya yi alwala sai ƙulli ɗaya ya warware, idan ya yi sallah sai ƙulli (ɗaya) ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai, inba haka ba sai ya wayi gari mai mummunar rai mai yawan kasala".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1142]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin Shaiɗan da kuma yakinsa ga mutumin da yake nufin tsayuwa dan sallar dare ko Asuba.
domin mumini idan ya tafi yin bacci shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙyaraysa - yana nufin: Ƙarshen kansa -.
Idan mumini ya farka kuma ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - bai amsa waswasin shaiɗan ba; sai ƙulli (ɗaya) ya warware.
Idan ya yi alwala sai ya warware. A
Idan ya tashi ya yi sallah sai ƙulli na uku ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai; dan farin cikinsa da abinda Allah Ya datar da shi na aikin ɗa'a, yana mai bushara da abinda Allah Ya yi masa alƙawari na lada da gafara, tare da abinda ya gushe daga gare shi na ƙulle-ƙullen Shaiɗan da nauyayawarsa, in ba haka ba zai wayi gari mai mummunan rai, mai baƙin ciki a zuciya, mai kasala daga ayyukan alheri da biyayya; domin cewa shi abin ɗaurewa ne da marin Shaiɗan, kuma abin nisanta daga kusancin Al-Rahman.