lis din Hadisai

Daga Humran bararran bawa na Usman Dan Affan cewa ya ga Usman Dan Affan ya nemi da akawo masa ruwan alwala, sai ya karkato da kwaryar (butar Alwala), sai ya wankesu sau uku, sannan ya shigar da (hannunsa na) dama a ruwan alwalar, sannan ya kuskure baki ya shaƙa ruwa ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, da hannayensa zuwa gwiwar hannaye sau uku, sannan ya shafi kansa, sannan ya wanke kowacce ƙafa sau uku, sannan ya ce: Na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya yi alwala irin wannan alwalar tawa, sai ya ce: "@Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu bai zantar da ransa a cikinsu ba, to, Allah Zai gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa*".
عربي Turanci urdu
"Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala"
عربي Turanci urdu
"Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".
عربي Turanci urdu
"Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa*, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
عربي Turanci urdu
Mun dawo tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Makka zuwa Madina har sai da muka kasance a wani ruwa a hanya, sai wasu mutane suka yi gaggawar (sallar) La'asar, sai suka yi alwala alhali suna gaggawa, sai muka kai gare su alhali karshen kafafuwanusu suna haske (lam’a) ruwa bai tabasu ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: @"Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala".
عربي Turanci urdu
"Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri*, idan dayanku ya farka daga baccinsa to ya wanke hannunsa kafin ya shigar da su a ruwan alwalarsa, domin cewa dayanku ba ya sanin a'ina hannunsa ya kasance". Lafazin Muslim: "Idan dayanku ya farka daga baccinsa kada ya nutsa hannunsa a cikin kwarya har sai ya wankesu sau uku, domin cewa shi ba ya sanin a'ina hannunsa ya sakance ".
عربي Turanci urdu
Idan kun sa shi, kuma idan kuna yin alwala, ku fara da kwanakinku.”
عربي Turanci urdu
Na halarci Amr dan Abu Hassan ya tambayi Abdullahi dan Zaid game da alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce a kawo masa kwarya ta ruwa, @sai ya yi musu alwala irin alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -* sai ya sanya hannunsa akwaryar, sai ya wanke hannayensa sau uku, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar, sai ya kuskure baki ya shaka ruwa ya face, kanfata uku, sannan ya shigar da hannunsa sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa sau biyu zuwa gwiwar hannu, sannan ya shigar da hannunsa sai ya shafi kansa, sai ya yi gaba da su ya yi baya sau daya, sannan ya wanke kafafuwansa zuwa idan sawu.
عربي Turanci urdu
Azabar wuta ta tabbata ga duga-dugai
عربي Turanci urdu
"Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci*, idan ya farka sai ya ambaci Allah, sai kulli ɗaya ya warware, idan ya yi alwala sai ƙulli ɗaya ya warware, idan ya yi sallah sai ƙulli (ɗaya) ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai, inba haka ba sai ya wayi gari mai mummunar rai mai yawan kasala".
عربي Turanci urdu
Mun kasance muna shirya wa Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - kayan aikin sa da tsarkake shi, saboda haka Allah zai aiko masa da duk abin da yake son ya aiko daga dare, don haka sai ya sa su daidai, ya yi alwala ya yi sallah.
عربي Turanci urdu
"Ba don kar in matsawa al'umma ta ba da ma umarce su da yin asuwaki yayin kowace salla"
عربي Turanci urdu
"Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa".
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Al-wala sai ya yi Alwala sai ya kuskure bakinsa, sannan ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau Uku,da hannunsa na Dama sau Uku, xayanma sau uku, kuma ya shafi kansa da Ruwa ba na ragowar hannunsa ba, kuma ya wanke Qafarsa har ya tsaftace ta
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Annabi SAW yayi Al-wala sai ya shafi tsakiyar kansa, da kuma kan Rawaninsa da Huffinsa
عربي Turanci urdu
Manzon Allah SAW ya kasance idan yayi Al-wala yakan kwaranya ruwa akan Damatsensa
عربي Turanci urdu
Babu Sallah ga duk wanda bashi da Al-wala, kuma babu Al-wala ga duk wanda bai anbaci sunan Allah ba a Al-walar
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasance yana wanka, da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu.
عربي Turanci urdu
"Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi"* Ya ce: Sai na ce: Ya mamakin kyan wannan, sai ga wani mai magana a gabana yana cewa: Wacce ke gabanta ta fi kyau, sai na duba sai ga Umar ya ce: Lallai ni na ganka ka zo ɗazu, ya ce: "Babu wani daga cikinku da zai yi alwala sai ya kai matuƙa - ko sai ya cika - alwalar sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne sai an buɗe masa kofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so".
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzon Allah SAW ya sunbanci Wata daga cikin Matansa, sannan ya futa Sallah kuma bai sake Alwala ba
عربي Turanci urdu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah*, sai na ce: Yaya kuka kasance kuna aikatawa? sai ya ce: Alwala tana isar ɗayanmu muddin dai bai yi kari (hadasi) ba.
عربي Turanci urdu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
عربي Turanci urdu
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu.
عربي Turanci urdu
"Idan ɗayanku ya ji wani abu a cikinsa, sai ya rikitar da shi cewa shin wani abu ya fita daga gare shi ko a'a, to, kada ya fita daga masallaci har sai ya ji kara ko ya ji waji wari".
عربي Turanci urdu
((Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al-kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala)).wanda ya sami damar tsawaita Farinsa daga gareku to ya aikata.Acikin wani Lafazi na Muslim:((Naga Aba Huraira yana Alwala,sai ya wanke Fuskarsa da Hannayensa har ya kusa isa Kafadunsa biyu,sannan ya wanke Kafafunsa biyu har saida ya daga izuwa Kaurinsa biyu,sannan yace:Na ji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al'kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala))wanda ya sami damar tsawaita Farinsa da kyalkyalinsa to ya aikata.Kuma acikin wani lafazin na Muslim:Na ji Badadina-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:((Adon Mumini yana kaiwa inda Alwala takai((.
عربي Turanci urdu
Mun kasance a lokacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba za mu sami irin wannan ba sai kadan, kuma idan mun same shi, ba mu da komai sai hannayenmu da bayanmu, da bayanmu.
عربي Turanci urdu
Duk wanda yake son yasan Al-walar Manzon Allah SAW to ita ce wannan
عربي Turanci urdu
Na kasance ɗan aiken Banul Muntafiƙi - ko a cikin jama'ar Bunul Muntafiƙi - zuwa wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Lokacin da muka zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bamu same shi agidansa ba, sai muka samu Nana A'isha uwar muminai, ya ce: Sai ta yi umarni a bamu farfesu, sai aka dafa mana, ya ce: Kuma aka zo mana da ƙina' - ƙina: Shi ne farantin da a cikinsa akwai dabino - sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «‌Shin kun samu wani abu ne? ko shin an yi umarni akawo muku wani abu ne?» ya ce: Mukace: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da mai kiwo ya kora tumakansa zuwa garke, atare da shi akwai wani 'yar akuya tana kuka, sai ya ce: «‌Kai wane me aka haifa maka?», ya ce: 'Yar akuya, ya ce: «‌To ka yanka mana babbar akuya a madadinta», Sannan ya ce: «‌Kada ka zaci» bai ce: kada ka zaci «‌Mu saboda kaine muka yankata ba, muna da tumakai ɗari, bama so su ƙaru, idan aka haifawa makiyayin 'yar akuya, sai mu yanka babbar akuya a madadinta» Ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai ni ina da wata mata, akwai wani abu a harshenta - yana nufin bata iya magana ba - ya ce: «‌To ka saketa», ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai sahabiya ce, kuma ina da ɗa tare da ita, ya ce: «‌To ka umarceta» Yana cewa ka yi mata wa'azi, «‌Idan akwai alheri a tare da ita zata aikata, kada ka daki matarka kamar yadda kake dukan baiwarka», sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labari game da alwala, ya ce: @«‌Ka cika alwala, ka tsettsefe tsakanin yatsu, ka kai matuƙa a kuskurar baki sai dai idan ka kasance mai azimi ne».
عربي Turanci urdu
Na ga Ammar Bn Yasir yayi Al-wala sai ya tsefe gemunsa, sai aka ce da shi: ko ya ce da shi: Ya kake tsefe Gemunka? ya ce: to mai zai hanani? kuma haqiqa naga Manzon Allah SAW yana tsefe Gemunsa
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Annabi SAW ya zo da xaya bisa Ukun Mudu sai yake shafawa a Dantsensa
عربي Turanci urdu
Sahabban Manzon Allah SAW sun Kasance a lokacinsa suna jiran Sallar isha har su fara gyangyaxi sannan suyi Sallah kuma basa sake Alwala
عربي Turanci urdu
Duk wanda yayi Wankan Gawa to yayi Wanka shi ma, kuma duk wanda ya xauketa to ya sake Alwala
عربي Turanci urdu
Lallai idanuwa Maxaurin Dubura ne, idan xayanku yayi bacci da idanuwansa to Maxauran zasu kwance ne
عربي Turanci urdu
"Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa* - idan ya wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa waɗanda hannayen sa suka damƙa tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa -, idan ya wanke ƙafafuwan sa kowane kuskuren da ƙafafuwan sa suka tafi gare shi zasu fita tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa - har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".
عربي Turanci urdu