عن أبي هريرة رضي الله عنه قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : ((إن أمتي يُدْعَون يوم القيامة غُرًّا مُحَجَلِّين من آثار الوُضُوء)). فمن اسْتَطَاع منكم أن يُطِيل غُرَّتَه فَليَفعل. وفي لفظ لمسلم: ((رأَيت أبا هريرة يتوضَّأ، فغسل وجهه ويديه حتى كاد يبلغ المنكبين، ثم غسل رجليه حتى رَفَع إلى السَّاقين، ثم قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: إنَّ أمتي يُدْعَون يوم القيامة غُرًّا مُحَجَّلِين من آثار الوُضُوء)) فمن استطاع منكم أن يطيل غُرَّتَه وتَحْجِيلَه فَليَفعَل. وفي لفظ لمسلم: سمعت خليلي صلى الله عليه وسلم يقول: ((تَبْلُغ الحِليَة من المؤمن حيث يبلغ الوُضُوء)).
[صحيح] - [الرواية الأولى: متفق عليه. الرواية الثانية: رواها مسلم. الرواية الثالثة: رواها مسلم]
المزيــد ...

((An karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi yace Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:((Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al-kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala)).wanda ya sami damar tsawaita Farinsa daga gareku to ya aikata.Acikin wani Lafazi na Muslim:((Naga Aba Huraira yana Alwala,sai ya wanke Fuskarsa da Hannayensa har ya kusa isa Kafadunsa biyu,sannan ya wanke Kafafunsa biyu har saida ya daga izuwa Kaurinsa biyu,sannan yace:Na ji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al'kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala))wanda ya sami damar tsawaita Farinsa da kyalkyalinsa to ya aikata.Kuma acikin wani lafazin na Muslim:Na ji Badadina-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:((Adon Mumini yana kaiwa inda Alwala takai((.
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi duka Riwar ta sa biyun

Bayani

Annabi tsira da aminci su tabbata agareshi yana yiwa Al'umarsa bushara da cewa hakika Allah maitsarki da daukaka yana kebantarsu da Alamar fifiko da daukaka ranar Alkiyama,a tsakanin Al'umai,ta yarda za'a kirawosu sai su zo agaban Halittu Fuskokinsu daHannayensu da Kafafuwansu suna kyalkyali na haske, wancananka gurbine daga guraben wannan Ibada maigirma,itace Alwala wacce suka dinga maimaitata abisa wannan Gabobi masu Alfarma don neman yardar Allah, da kuma neman ladansa, sai sakamakonsu ya kasance wannan girmamawar maigirma kebantacciya.Sannan Abu Huraira Allah ya yarda dashi yake cewa: "Wanda ya sami ikon tsawaita wannan Fari to ya aikata" domin cewashi duk sanda ya tsawaita bigiran wankewa daga Gaba Fari da kyalkyali zai karu, domin cewa adon Hasken yana kaiwa inda Ruwan Alwala ya kai, sai dai abin shar'antawa kawai wanke Hannaye biyu acikin Alwala ya zama zuwa gwiwar Hannaye biyu ya shigar da gwiwar da farawa da Dantse da wanke wani yanki daga gareshi, da kuma wanke Diga Digai biyu izuwa Idon sawaye biyu ya shigar da Idon sawayen biyu da farawa da kauri, kuma ba'a shara'anta wanke Dantse da kauri acikin Alwala ba

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin