عن أبي هريرة رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم : "لاَ يَقْبَل الله صلاَة أَحَدِكُم إِذا أَحْدَث حَتَّى يَتوضَّأ".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah ya yarda dashi, zuwa ga Annabi: Allah ba zai karbi sallar wanda ya yi kari ba har sai ya yi alwala
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Allah Mai hikima yana nusar da mu game da sha'anin sallah , kada a yi ta sai a cikin kyakkyawan kamanni, domin itace alaka mai karfi tsakanin Ubangiji da bawansa, itace hanyar tsira, don haka ya umarce shi da yin alwala da tsarki yayin da za'a yi ta, kuma ya gaya masa cewa sallar da babu tsarki baza a karbeta ba