عَنْ مُصْعَبِ بْنِ سَعْدٍ قَالَ: رَأَى سَعْدٌ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ لَهُ فَضْلًا عَلَى مَنْ دُونَهُ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«هَلْ تُنْصَرُونَ وَتُرْزَقُونَ إِلَّا بِضُعَفَائِكُمْ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 2896]
المزيــد ...
Daga Mus'ab ɗan Sa'ad ya ce: Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ga cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2896]
Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya yi zatan cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi daga raunana saboda gwarzantakarsa da makamancin haka! Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin ana taimakonku ne kuma ana azirtaku ai sai saboda raunananku ta hanyar addu'o'insu da sallalolinsu da ikhlasinsu; domin su a galibi su ne mafi tsananin ikhlasi a cikin addu'a, kuma mafi yawan khushu'i a cikin ibada dan wofintar zuciyarsu daga rataya da ƙawace-ƙawacen duniya.