عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ زَيْدٍ رضي الله عنه:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ تَوَضَّأَ مَرَّتَيْنِ مَرَّتَيْنِ.
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 158]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi -:
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 158]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a wasu lokutansa idan zai yi alwala yana wanke Kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalarsa sau biyu, sai ya wanke fuska - daga cikin wankewar akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa - da hannaye da ƙafafuwa sau biyu.