عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ:
تَوَضَّأَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَرَّةً مَرَّةً.
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 157]
المزيــد ...
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 157]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a sashin lokutansa idan zai yi alwala sai ya wanke kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalarsa sau ɗaiɗai, sai ya wanke fuska - daga [cikin wanke fuska] akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa - da hannaye da ƙafafuwa sau ɗaiɗai, wannan shi ne gwargwadon wajibi.