عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا وَجَدَ أَحَدُكُمْ فِي بَطْنِهِ شَيْئًا، فَأَشْكَلَ عَلَيْهِ أَخَرَجَ مِنْهُ شَيْءٌ أَمْ لَا، فَلَا يَخْرُجَنَّ مِنَ الْمَسْجِدِ حَتَّى يَسْمَعَ صَوْتًا، أَوْ يَجِدَ رِيحًا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 362]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan ɗayanku ya ji wani abu a cikinsa, sai ya rikitar da shi cewa shin wani abu ya fita daga gare shi ko a'a, to, kada ya fita daga masallaci har sai ya ji kara ko ya ji waji wari".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 362]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -yana bayyana cewa idan wani abu ya yi kai-kawo a cikin cikin mai sallah, sai ya rikitar da shi; shin wani abu ya fita daga gareshi ko a'a? to, kada ya fita daga sallarsa ya yanketa don sake alwala, har sai ya tabbatar da samun karin da ya ɓata alwalarsa; ta hanyar ya ji karar tusa, ko ya ji wari; domin abin aka tabbatarw to kokwanto ba ya ɓata shi, shi tabbas ya tabbatar da tsarki (alwala) kari kuma akwai kokwantone a cikinsa.