+ -

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«لَا ضَرَرَ وَلَا ضِرَارَ، مَنْ ضَارَّ ضَرَّهُ اللَّهُ، وَمَنْ شَاقَّ شَقَّ اللَّهُ عَلَيْهِ».

[صحيح بشواهده] - [رواه الدارقطني] - [سنن الدارقطني: 3079]
المزيــد ...

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa".

[Ingantacce ne a baki dayan Riwayoyin sa] - [Al-Dar Al-Kutni Ya Rawaito shi] - [سنن الدارقطني - 3079]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, baya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida.
Kuma ba ya halatta gareshi ya fukanci cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta sai dai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba.
Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana narko da faruwar cuta ga wanda yake cutar da mutane, da kuma faruwar wahala ga wanda yake tsanantawa mutane.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani game da ramuwa da sama da abin da aka yi.
  2. Allah bai umarci bayainsa da wani abu da zai cutar da su ba.
  3. Haramta cuta da cutarwa ta magana ko da aiki ko da bari.
  4. Sakamako yana kasancewa daga jinsin aiki, wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cuta, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawa.
  5. Daga ƙa'idojin shari'a akwai: "Cuta ana gusar da ita", shari'a ba ta tabbatar da cuta, kuma tana inkarin cutarwa.