+ -

عَنِ ابنِ مَسعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا يَحِلُّ دَمُ امْرِئٍ مُسْلِمٍ إِلَّا بِإِحْدَى ثَلَاثٍ: الثَّيِّبُ الزَّانِي، وَالنَّفْسُ بِالنَّفْسِ، وَالتَّارِكُ لِدِينِهِ المُفَارِقُ لِلْجَمَاعَةِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1676]
المزيــد ...

Daga Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku, bazawarin da ya yi zina, da ran (da ya kashe) rai, da wanda ya bar addininsa wanda ya bar jama'a».

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1676]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa jinin musulmi haramun ne, sai dai idan ya aikata ɗaya daga cikin ɗabi'un nan uku: Na farko: Wanda ya faɗa cikin alfashar zina, alhali ya riga ya yi aure da ƙulla ingantaccen ɗaurin aure, to sai kashe shi ta hanyar jifa ya halatta. Na biyu: Wanda ya kashe tsararren rai da aka hana kashewa ba tare da wani haƙƙi ba, to sai a kashe shi da sharuɗɗansa. Na uku: Wanda ya fita daga cikin jama'ar muslmai; ko dai ta hanyar barin addininsa gabaɗayansa ta hanyar yin ridda, ko wanda ya bari ba tare da ridda ba ta hanyar barin sashinsa kamar 'yan tawaye, da 'yan fashi, da mayaƙa cikin Khwarij da wasunsu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin aikata waɗannan ɗabi'un uku, kuma wanda ya aikata ɗaya daga cikinsu ya cancanci uƙubar kisa; ko dai kafirci, shi ne yin ridda daga Musulunci, ko kuma haddi, sune: Bazawarin da ya yi zina, da wanda ya yi kisa da gangan.
  2. Wajabcin kiyaye mutunci da kuma tsarkake shi .
  3. Wajabcin girmama musulmi, kuma jininsa a tsare yake.
  4. Kwaɗaitarwa akan lazimtar jama'ar musulmai da kuma rashin rabuwa da su.
  5. Kyakkyawan koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda wani lokaci zancensa yake zuwa da rarrabewa; domin rarrabewar tana taƙaita mas'aloli kuma tana tattarosu, kuma shi ne mafi saurin haddacewa.
  6. Allah Ya shara'anta haddodi; dan tsawatar da masu laifi, da kuma kare zamantakewa da kiyayewa daga manyan laifuka.
  7. zartar da waɗannan hukunce hukuncen ya rataya ne akan shugaba ne kadai.
  8. Dalilan dake sa a yi kisa sun fi uku, sai dai basa fita daga wadannan ukun, Ibnul Arabi al-Maliki ya ce: Ba sa fita daga waɗanannan ukun ta kowane irin hali, domin duk wanda ya yi asiri, ko ya zagi Annabin Allah to ya kafirta, shi ya shiga cikin wanda ya bar addininsa.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili bushtu Albaniyanci الغوجاراتية النيبالية الليتوانية الدرية الصربية الطاجيكية المجرية التشيكية Kanadische Übersetzung الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية الخميرية
Manufofin Fassarorin