عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ أَصَابَ حَدًّا فَعُجِّلَ عُقُوبَتَهُ فِي الدُّنْيَا فَاللَّهُ أَعْدَلُ مِنْ أَنْ يُثَنِّيَ عَلَى عَبْدِهِ العُقُوبَةَ فِي الآخِرَةِ، وَمَنْ أَصَابَ حَدًّا فَسَتَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ وَعَفَا عَنْهُ فَاللَّهُ أَكْرَمُ مِنْ أَنْ يَعُودَ فِي شَيْءٍ قَدْ عَفَا عَنْهُ».
[حسن] - [رواه الترمذي وابن ماجه] - [سنن الترمذي: 2626]
المزيــد ...
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Wanda ya aikata laifin da za'a iya yi masa haddi sai aka gaggauto da uƙubarsa a duniya to Allah Shi ne Mafi karamcin Ya yi wa bawanSa uƙuba (biyu, daya aduniya da kuma) a lahira, wanda ya aikata laifin da za’a yi masa haddi sai Allah Ya suturta shi kuma Ya yi masa afuwa to Allah Shi ne Mafi karamcin ya dawo da abinda Ya riga Ya yi afuwarsa».
[Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 2626]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya aikata wani saɓon da yake wajabta haddin shari'a, kamar zina da sata, sai ya samu uƙubarsa kuma aka tsayar masa da haddi a duniya, to lallai hakan zai shafe masa wannan saɓon, kuma zai shafe uƙubarsa ta lahira; domin cewa Allah Shi ne Mafi karamci kuma Mafi jin ƙan ya haɗawa bawanSa uƙuba biyu. Wanda kuma Allah Ya suturta shi a duniya, ba a yi masa uƙuba ba akan wannan saɓon, kuma Allah Ya yi masa afuwa Ya gafarta masa, to Allah Shi ne Mafi buwaya kuma Mafi girma Mafi karamcin ya dawo da uƙubar zunubin da Ya riga Ya gafarta shi kuma Ya yi afuwarsa.