عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، وَكَانَ شَهِدَ بَدْرًا، وَهُوَ أَحَدُ النُّقَبَاءِ لَيْلَةَ العَقَبَةِ: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ، وَحَوْلَهُ عِصَابَةٌ مِنْ أَصْحَابِهِ:
«بَايِعُونِي عَلَى أَلَّا تُشْرِكُوا بِاللَّهِ شَيْئًا، وَلاَ تَسْرِقُوا، وَلاَ تَزْنُوا، وَلاَ تَقْتُلُوا أَوْلاَدَكُمْ، وَلاَ تَأْتُوا بِبُهْتَانٍ تَفْتَرُونَهُ بَيْنَ أَيْدِيكُمْ وَأَرْجُلِكُمْ، وَلاَ تَعْصُوا فِي مَعْرُوفٍ، فَمَنْ وَفَى مِنْكُمْ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ، وَمَنْ أَصَابَ مِنْ ذَلِكَ شَيْئًا فَعُوقِبَ فِي الدُّنْيَا فَهُوَ كَفَّارَةٌ لَهُ، وَمَنْ أَصَابَ مِنْ ذَلِكَ شَيْئًا ثُمَّ سَتَرَهُ اللَّهُ فَهُوَ إِلَى اللَّهِ، إِنْ شَاءَ عَفَا عَنْهُ وَإِنْ شَاءَ عَاقَبَهُ» فَبَايَعْنَاهُ عَلَى ذَلِكَ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 18]
المزيــد ...
Daga Ubada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - , kuma ya kasance ya halarci Badr, shi yana daga cikin jagorori a daren Aƙabah: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce alhali a gefensa akwai wasu jama'a daga sahabbansa:
«Ku yi mini caffa akan kada ku taranya wani da Allah (a bauta), kada ku yi sata, kada ku yi zina, kada ku kashe 'ya'yanku, kada kuzo da ƙirƙiren ƙaryar da zaku aikata ta tsakanin hannayenku da ƙafafuwanku, kuma kada ku saɓa a wani aikin alheri, to wanda ya aikata a cikinku to ladansa yana wurin Allah, wanda ya aikata wani abu daga hakan (saɓo) sai aka yi masa uƙuba a duniya to shi kaffarane a gare shi, wanda kuma ya aikata wani abu daga hakan (saɓo) sannan Allah Ya suturta shi to shi yana ga Allah, idan Ya so zai yi masa rangwami idan kuma Ya so Ya yi masa uƙuba» sai muka yi masa caffa (mubaya’a) akan hakan.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 18]
Ubada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, kuma ya kasance yana daga waɗanda suka halarci yaƙin Badr babba, kuma shi ne jagoran mutanensa waɗanda suka gabato dan yin caffa don taimakon Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a daren Aƙaba wacce ke Mina - a lokacin da Manzo ya kasance a Makka kafin Hijirarsa zuwa Madina - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana zaune tsakanin sahabbansa sai ya nemi su yi masa alƙawari akan wasu al'amura: Na farko: Kada su taranya wani abu da Allah a bautar Allah ko da ya ƙaranta. Na biyu: Kada su yi sata. Na uku: Kada su aikata zina. Na huɗu: Kada su kashe 'ya'yansu; mazansu dan jin tsoron talauci ko matansu dan jin tsoron aibi. Na biyar: Kada su yi ƙaryar da zasu ƙirƙireta tsakanin hannayensu da ƙafafuwansu inda mafi yawancin ayyuka suna afkuwa ne ta su koda ragowar gaɓɓai sun yi tarayya da su (a ciki). Na shida: Ba za su saɓawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba a cikin wani aikin alheri. Wanda ya tabbata a cikinsu akan alƙawarin kuma ya lazimci hakan to ladansa yana ga Allah, wanda kuma ya aikata wani abu daga abinda aka ambata - banda shirka - sai aka yi masa uƙuba saboda shi a duniya ta hanyar tsaida haddi a kansa to shi kaffara ne gare shi kuma da shi ne zunubi ya saraya, kuma wanda ya aikata wani abu sannan Allah Ya suturta shi to al'amarinsa yana ga Allah; idan Ya so zai yi masa afuwa idan kuma Ya so zai yi masa uƙuba, sai duk waɗanda ke gurin suka yi masa caffa (mubaya’a) akan hakan.