+ -

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ بُسْرٍ رضي الله عنه أَنَّ رَجُلاً قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ إِنَّ شَرَائِعَ الإِسْلاَمِ قَدْ كَثُرَتْ عَلَيَّ، فَأَخْبِرْنِي بِشَيْءٍ أَتَشَبَّثُ بِهِ، قَالَ:
«لاَ يَزَالُ لِسَانُكَ رَطْبًا مِنْ ذِكْرِ اللَّهِ».

[صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 3375]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Busr - Allah Ya yarda da shi - cewa wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah lallai shari'un musulunci haƙiƙa sun yi mini yawa, ka sanar dani wani abu wanda zan rataya da shi, sai ya ce:
"Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah".

[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 3375]

Bayani

Wani mutum ya kai ƙara wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa nafilifilin ibadu sun yi masa yawa har ya gajiya daga yin su saboda rauninsa, sannan ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi ga wani aiki mai sauki mai jawo lada mai yawa wanda zai rataya da shi ya yi riƙo da shi.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nunar masa harshensa ya zama ɗanye mai motsawa saboda dawwamar ambatan Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - a kowane lokaci da hali; na tasbihi da tahmidi da istigafari da addu'a da makamancin hakan.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar dawwama akan ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
  2. Daga girman falalar Allah (akwai) sawwaƙe sabubban lada.
  3. Fifikon bayi a rabonsu daga ƙofofin aikin lada da alheri.
  4. Yawan ambatan Allah da harshe tasbihi da tahmidi da hailala da kabbara da wanin hakan tare da dacewar zuciya yana tsayawa matsayin yawa da yawan nafilifilin ayyukan ɗa'a.
  5. Lurarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga masu tambaya da amsawa kowa da abinda ya dace da shi.