عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قالَ:
«لاَ يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ، حَتَّى يُحِبَّ لِأَخِيهِ مَا يُحِبُّ لِنَفْسِهِ».  
                        
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 13]
                        
 المزيــد ... 
                    
Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ɗayanku ba zai yi  imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa". 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 13]                                            
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa imani cikakke ba ya tabbata ga wani daga musulmai har sai ya so wa ɗan'uwansa abinda yake sowa kansa na ayyukan ɗa'a da nau'ukan alkairai a addini da rayuwa, kuma ya ki abinda yake ki ga kansa, idan ya ga wata tawaya ga ɗan'uwansa musulmi a addininsa, to ya yi kokari a cikin gyarata, idan ya ga wani alheri a cikinsa to ya daidaita shi ya taimake shi, ya yi masa nasiha a al'amarin Addininsa da duniyarsa.