عن أبي ذر رضي الله عنه قال: قال لي النبي صلى الله عليه وسلم:
«لَا تَحْقِرَنَّ مِنَ الْمَعْرُوفِ شَيْئًا، وَلَوْ أَنْ تَلْقَى أَخَاكَ بِوَجْهٍ طَلْقٍ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2626]
المزيــد ...

Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi -ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce da ni:
"Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [Sahih Muslim - 2626]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya kwaɗaitar a kan aikin alheri, kuma kada ya wulaƙantashi ko da ya kasance kaɗan ne, daga wannan (akwai) sakin fuska ta hanyar murmushi a yayin haɗuwa, to, yana kamata ga musulmi ya yi kwaɗayi a kansa; saboda abin da ke cikinsa na ɗebe kewa ga ɗan uwa musulmi da shigar da farin ciki gareshi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar soyayya a tsakanin muminai da murmushi da walwala a yayin haɗuwa.
  2. Cikar wannan shari'ar da tattarowarta, kuma ita ta zo da dukkanin abin da a cikinsa akwai gyara musulmai da haɗe kansu.
  3. Kwaɗaitarwa a kan aikata aikin alheri ko da ya ƙaranta.
  4. An so shigar da farin ciki ga musulmai; saboda abin da ke cikin hakan na tabbatar da sabo a tsakaninsu.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (67)