+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا تَبْدَؤوا الْيَهُودَ وَلَا النَّصَارَى بِالسَّلَامِ، فَإِذَا لَقِيتُمْ أَحَدَهُمْ فِي طَرِيقٍ فَاضْطَرُّوهُ إِلَى أَضْيَقِهِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2167]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Kada ku farawa Yahudawa ko Nasara da sallama, idan kun haɗu da ɗayansu a hanya to ku buƙace shi zuwa mafi ƙuncinta".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2167]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga farawa Yahudawa da Nasara da sallama koda sun kasance kafiran amana ne, ballantana wasunsu cikin kafirai, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mu idan mun haɗu da ɗayansu a wata hanya to mu buƙace shi zuwa mafi ƙuncin hanyar, to mumini shi ne wanda yake tafiya a tsakiyar hanya, wanda yake nesa (da hanya) shi ne kafiri, kuma musulmi ba ya kasancewa ƙasƙantacce da wani hali daga halaye.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الرومانية Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ba ya halatta ga musulmi ya fara wa wani daga Yahudawa da Nasara da wasunsu daga kafirai da sallama.
  2. Maida sallama gare su yana halatta idan sun fara sallamar shi ne ya ce: Wa'alaikum.
  3. Ba ya halatta ga musulmi ya nufi cutar da kafiri, shi ne ya ƙuntata masa dan nufi ba tare da wani dalili ba; dan ya buƙace shi zuwa mafi ƙuncin hanya; sai dai idan hanyar ta kasance mai ƙunci ce ko mai cunkoso to musulmi shi ne mafi cancanta da ita, kafiri yana nesa da ita.
  4. Bayyanar da ɗaukakar musulmai da ƙasƙantar da wasunsu, ba tare da zalinci ko munana magana ba.
  5. Ƙuntatawa akan kafirai dan abinda suke akansa na kafirce wa Allah - Maɗaukakin sarki -, zai iya zama sababi a musuluntar su; sai su tsira daga wuta, idan hakan ya ɗauke su akan sanin sababi.
  6. Babu laifi musulmi ya ce wa kafiri tun a farko yaya kake, an tashi lafiya, an wuni lafiya? da makanmancin wannan idan buƙata ta yi kira zuwa hakan; domin hanin abin ɗauka ne akan aminci.
  7. Al-Ɗaibi ya ce: Abin zaɓi cewa ɗan bidi'a ba'a fara masa sallama, koda ya yi sallama ga wanda bai san shi ba sai ya bayyana cewa kafirin amana ne ko ɗan bidi'a ne sai ya ce: Na janye sallama ta, dan wulaƙanta shi.