عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«كُلُّ مَعْرُوفٍ صَدَقَةٌ».
[صحيح] - [رواه البخاري من حديث جابر، ورواه مسلم من حديث حذيفة] - [صحيح البخاري: 6021]
المزيــد ...
Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Kowa ne aikin alheri sadaka ne".
[Ingantacce ne] - - [صحيح البخاري - 6021]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin kyautatawa da amfani ga wasu na magana ne, ko na aiki yana zama sadaka, kuma a cikinsa akwai lada da sakamako.