عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«لَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ قُبُورًا، وَلَا تَجْعَلُوا قَبْرِي عِيدًا، وَصَلُّوا عَلَيَّ؛ فَإِنَّ صَلَاتَكُمْ تَبْلُغُنِي حَيْثُ كُنْتُمْ».
[حسن] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 2042]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada ku maida gidajanku kaburbura, kuma kada ku maida kabari na idi, ku yi salati a gareni; domin cewa salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke".
[Hasan ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 2042]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah sai su zama kamar makabartu, da ba'a sallah a cikin su. Kuma ya yi hani daga maimaita ziyarar wani kabari da taruwa a wurinsa ta fuskar al'ada; domin hakan hanya ce zuwa ga shirka, Ya yi umarni da yin salati da sallama a gare shi a kowane wuri anan doron kasa; domin cewa hakan yana isa gare shi daga na kusa da na nesa duk daya ne, babu bukatuwa zuwa kaikawo a kabarinsa.