عن أم سلمة رضي الله عنها قالت: «جاءت أمُّ سُلَيمٍ امرأةُ أَبِي طَلحة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فقالت: يا رسول الله، إنَّ الله لا يَسْتَحيِي من الحَقِّ، فهل على المرأة من غُسْلٍ إِذَا هِيَ احْتَلَمَت؟ فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : نعم، إِذَا رَأَت المَاء».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Ummusalama -Allah ya yarda da ita- tace:"Ummu Sulaim Matar Abi Dalha ta zo wajen Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- tace:"Ya Manzon Allah, Allah baya jin kunya game da gaskiya,shin mace zata yi wanka idan tayi mafarki?sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah- yace: Eh, zata yi amma in ta ga ruwa."
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Ummu Sulai 'Yar Madina -Allah ya yarda da ita- ta zo wajen Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- don ta tambaye shi,kasancewar tambayar na da alaka da matunci,akan ji kunyar fada,shi ne ta fara gabatar da yan kalmomin don yin shimfida ga tambayar ta. Sai tace: Allah Madukaki shi ne Gaskiya,bai hana ambaton gaskiya,in dai akwai wani amfani cikin tambayar,bayan Ummu Sulaim ta gabatar da wannan shimfida,sai ta fadi tambayarta kai tsaye,tace:shin mace zata yi wanka in tayi mafarki ana saduwa da ita?Sai Annabi tsira da aminci yace,za ta yi wanka indai har ta ga mani.