عَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا تَقُولُوا: مَا شَاءَ اللهُ وَشَاءَ فُلَانٌ، وَلَكِنْ قُولُوا: مَا شَاءَ اللهُ ثُمَّ شَاءَ فُلَانٌ».
[صحيح بمجموع طرقه] - [رواه أبو داود والنسائي في الكبرى وأحمد] - [السنن الكبرى للنسائي: 10755]
المزيــد ...
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya so, saidai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so".
- - [السنن الكبرى للنسائي - 10755]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya ce a zancensa: Allah Ya so wane ma ya so", ko Allah Ya so da wane; hakan domin ganin damar Allah da nufinSa a wawaice suke, wani ba ya tarayya daShi a cikinsu, a cikin amfani da Waw (da) a adafi alamtarwa ne na hada wani tare da Allah da daidaitawa a tsakaninsu. Saidai ya ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so, Sai ya sanya ganin damar bawa mai bi ce ga ganin damar Allah ta hanyar fadin: "Sannan" canjin "da"; domin "sannan" tana fa'idantar da bibiya da kuma jinkiri.