عن ميمونة بنت الحارث رضي الله عنها قالت: "وَضَعتُ لِرسولِ الله صلى الله عليه وسلم وَضُوءَ الجَنَابَة، فَأَكفَأ بِيَمِينِهِ على يساره مرتين -أو ثلاثا- ثم غَسَل فَرجَه، ثُمَّ ضَرَب يَدَهُ بالأرضِ أو الحائِطِ مرتين -أو ثلاثا- ثم تَمَضْمَضَ واسْتَنْشَقَ، وَغَسَلَ وَجهَه وذِرَاعَيه، ثُمَّ أَفَاضَ على رَأسِه الماء، ثم غَسَل جَسَدَه، ثُمَّ تَنَحَّى، فَغَسَل رِجلَيه، فَأَتَيتُه بِخِرقَة فلم يُرِدْهَا، فَجَعَل يَنفُضُ الماء بِيَده".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Maimuna 'Yar Haris -Allah ya yarda da ita- Tace: "Na kaiwa Annabi -tsira da amincin Allah- ruwan wankan janaba,sai ya karkata shi da hannun damansa ya zuba ruwa a hannun hagunsa sau biyu -ko sau uku- sannan ya wanke gabansa,sannan ya buga hannunsa a kasa ko a jikin katanga sau biyu -ko sau uku- sannan ya kurkure baki ya shaka ruwa,ya wanke fuskarsa da zira'insa biyu,sannan ya kwara ruwa a kansa,sannan ya wanke jikinsa,sannan ya duka,ya wanke kafafunsa,sai nazo masa da yankin yadi,bai karba ba sai ya fara sharce ruwa da hannunsa.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Maimuna 'Yar Haris Uwar muminai -Allah ya yarda da shi- na bayyana mana wani salo daga salon wankan janabar Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-a inda ta kai masa ruwa don yayi wankan janaba,sai yayi amfani da hannun damansa ya zuba ruwa kan hannun hagun dinsa,ya wanke su sau biyu ko sau uku,sannan ya tsaftace gabansa ta hanyar wanke shi don gusar da dattin janaba,sai ya bugi kasa ko katanga da hannunsa ya cuccuda su sau biyu ko sau uku,ya kurkure bakinsa yayi shaka ya kuma wanke fuskarsa da hannayensa,sannan ya kwara ruwa a kansa,sannan ya wanke sauran jikinsa,sannan ya canja waje ya wanke kafafuwansa a inda ya koma,sannan tazo masa da tawul don ya tsane jikinsa,sai ya gwammace ya sharce da hannunsa,don haka yaki karbar tawul din.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Swahili الدرية
Manufofin Fassarorin