عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: « تَمَتَّعَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم فِي حَجَّةِ الوَدَاع بالعُمرَة إلى الحج وأهدَى، فَسَاقَ مَعَهُ الهَدْيَ مِن ذِي الحُلَيفَة، وَبَدَأَ رَسول اللَّهِ صلى الله عليه وسلم وَأَهَلَّ بالعمرة، ثُمَّ أَهَلَّ بالحج، فَتَمَتَّعَ النَّاس مع رسول اللَّهِ صلى الله عليه وسلم فَأَهَلَّ بالعمرة إلَى الحج، فَكَان مِن النَّاس مَنْ أَهْدَى، فَسَاقَ الهَدْيَ مِن ذي الحُلَيفَة، وَمِنهُم مَنْ لَمْ يُهْدِ، فَلَمَّا قَدِمَ رسول اللَّه صلى الله عليه وسلم قَالَ للنَّاس: مَنْ كَانَ مِنكُم أَهْدَى، فَإِنَّهُ لا يَحِلُّ مِن شَيء حَرُمَ مِنْهُ حَتَّى يَقْضِيَ حَجَّهُ، وَمَن لَم يَكُن أَهْدَى فَلْيَطُفْ بالبَيت وَبالصَّفَا وَالمَروَة، وَلْيُقَصِّر وَلْيَحْلِل، ثُمَّ لِيُهِلَّ بالحج وليُهدِ، فَمَن لم يجد هَدْياً فَلْيَصُم ثَلاثَةَ أَيَّام فِي الحج وَسَبعة إذَا رَجَعَ إلى أَهلِهِ فَطَافَ رسول اللَّهِ صلى الله عليه وسلم حِينَ قَدِمَ مَكَّةَ، وَاستَلَمَ الرُّكْنَ أَوَّلَ شَيْءٍ، ثُمَّ خَبَّ ثَلاثَةَ أَطْوَافٍ مِنْ السَّبْعِ، وَمَشَى أَربَعَة، وَرَكَعَ حِينَ قَضَى طَوَافَهُ بالبيت عِند المَقَام رَكعَتَين، ثُمَّ انصَرَفَ فَأَتَى الصَّفَا، وطاف بِالصَّفَا وَالمَروَة سَبعَةَ أَطوَاف، ثُمَّ لَم يَحلِل مِنْ شَيْءٍ حَرُمَ منه حَتَّى قَضَى حَجَّهُ، وَنَحَرَ هَدْيَهُ يوم النَّحرِ، وَأَفَاضَ فَطَافَ بالبيت، ثُمَّ حَلَّ مِن كُلِّ شَيء حَرُمَ مِنهُ، وَفَعَلَ مِثل مَا فَعَلَ رَسول اللَّه صلى الله عليه وسلم : مَن أَهدَى وَسَاقَ الهَديَ مِن النَّاسِ». «رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم حِينَ يَقْدَمُ مكَّة إذا اسْتَلَمَ الرُّكْنَ الأَسْوَدَ -أَول ما يَطُوفُ- يَخُبُّ ثَلاثَةَ أَشْوَاطٍ».
[صحيح] - [متفق عليه بروايتيه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda dasu- yace: "Manzo Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya yi tamattu'i a Hajjinsa ta bankwana yayi umara yayi hajji kuma yayi hadaya. Ya taho da abin hadayar daga Zulhulaifa. Sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah- ya fara yin umara, sannan yayi hajji, sai mutane suka yi tamattu'i tare da Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi suka fara yin umara sannan hajji, daga mutane akwai wanda suka yi hadaya, suka taho da abin hadayar daga Zulhulaifa, wasu kuma basu yi hadayar ba, yayin da Manzon Allah tsira da aminci yazo sai yace da mutane Duk wanda yayi hadaya a cikinku, to duk abin da ya haramta a gare shi to baya halarta har sai ya gama hajjinsa, wanda kuma bai yi hadaya ba to yayi dawafi yayi safa da marwa, ya rage gashi, sannan ya kwance, sannan ya yi hajji kuma ya yi hadaya, wanda bai sami abin yin hadaya ba to yayi azumi uku lokacin hajji ko yayi bakwai idan ya koma garinsu, sai Manzo -tsira da aminci su tabbata a gare shi- yayi dawafi yayin da yazo Makka, ya sumbaci Rukni da farko, sannan yayi dawafi uku da sauri, sauran hudun kuma yayi tafiya a cikinsu, yayi salla raka'a biyu a Makama Ibrahim bayan ya gama dawafinsa, sannan ya yi Safa da Marwa sau bakwai, sannan bai yi wani abu da ya haramta a gare shi ba har sai da ya kammala hajjinsa, ya soke hadaya a ranar sokewa, kuma yayi Dawafin Ifadwa, sannan ya halarta duk abin da ya haramta gare shi a halin gabatar da ibadar, sai wadanda sukayi hadaya suka yi irin duk abin da Manzo -tsira da amincin Allah- ya aikata, "Na ga Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi lokacin da yazo Makka in ya sumbaci Arruknul Aswad -farkon dawafi- yana sauri a zagaye uku".
Ingantacce ne - Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin sa

Bayani

Yayin da Annabi -tsira da amincin Allah- ya fita izuwa Zulhulaifa " Mikatin Mutanen Madina" don yin Hajjinsa ta bankwana, yayi bankwana da Dakin Allah yayi bankwana da mutane, yayi bankwana da Aikin hajjin, kuma ya shaidar da cewa ya isar da sakon Allah zuwa ga mutane, sai ya daura haramin yin umara da hajji, sai yayi kirani, Kirani shi ne Tamattu'i, sai mutane suka yi tamattu'i tare da Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi- wasu suka yi haramar yin umra da hajji gaba daya, wasu kuma suka yi haramar yin umara, tare da niyyar yin hajji bayan sun gama umra, wasu kuma suka yi niyyar yin hajji kadai,Annabi -tsira da amincin Allah ya basu zabi tsakanin abu ukun, Annabi tsira da aminci da wasu daga sahabbai suka taho da hadayarsu daga Zulhulaifa, wasu kuma basu taho da ita ba, yayin da suka kusa da Makka sai Annabi tsira da amincin Allah ya kwadaitar da wadanda suke ifradi da masu kirani amma basu taho da hadaya ba su mayar da niyyarsu ta yin umara, bayan sunyi dawafi da saayi sai yace su yi saisaye, su warware umararsu sannan suyi harramar hajji kuma suyi hadaya, saboda yin umara da hajji a tafiya daya, wanda kuma bashi da hadaya, to yayi azumi goma, uku a can bakwai kuma in ya koma garinsu.Lokacin da Annabi tsira da amincin Allah yazo Makka sai ya sumbaci Rukni, yayi dawafi bakwai, yayi uku da sauri kasancewar sune na farko bayan zuwansa, yayi hudu a hankali, sannan yayi salla raka'a biyu a Makamu Ibrahim, sannan yayi Safa da Marwa sau bakwai, yana yin sassarfa a tsakanin alamomi biyu, yayi tafiya a inda ba nan ba, kuma bai kwance haraminsa ba har sai da ya gama hajji, ya soke hadayarsa ranar sokewa, bayan ya gama hajjinsa ya jefi Jamrat Al'akba, ya soke hadayarsa, ya aske kansa. Wannan shine tahalluli na farko, sai yayi dawafin ifadwa, sannan ya halarta komai, harma da kusantar iyali, duk sahabban da suka zo da hadaya suma suka yi haka.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Portuguese
Manufofin Fassarorin