+ -

عن عبد الله بن عبَّاس رضي الله عنهما قال: «أُمِرَ الناس أن يكون آخر عَهْدِهِمْ بالبيت، إلا أنه خُفِّفَ عن المرأة الحائض».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da su- yace: "An umarci mutane dasu yi dawafi ga dakin Allah a karshe,sai dai anyi sauki ga mace mai haila".
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Dakin Ka'aba yana da daraja da daukaka,kuma shi wata alama ce ta bautar Allah da kankan da kai da tsoron Allah,kuma yana da kwarjini a zukatan mutane,rayuka sun damfaru da shi,suna son shi.Don haka Annabi ya umarci mahajjaci daya sanya dawafi ga dakin Allah abu na karshe,ya zama ban kwana,sai dai anyi sauki ga mace mai haila don gudun kar ta bata masallacin.wannan kuma ya shafi Hajji ne kawai banda Umra.Duba littafin Taisiril Allam,Tanbihul Afham,Ta'asisil Ahkam.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili
Manufofin Fassarorin