عَنْ أُمِّ عَطِيَّةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ:
نُهِينَا عَنِ اتِّبَاعِ الجَنَائِزِ، وَلَمْ يُعْزَمْ عَلَيْنَا.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1278]
المزيــد ...
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
An hanamu bin jana'iza, amma ba'a ƙarfafa hanin a kanmu ba.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1278]
Ummu Aɗiyya al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana mata bin jana'iza; hakan saboda abinda ake jin tsoro a cikin hakan na fitina garesu da kuma fitinuwa da su, da kuma ƙarancin haƙurinsu, sannan Allah Ya yarda da ita ta bada labarin cewa bai ƙarfafa hanin ba kamar yadda yake aikatawa a sauran abubuwan da ya hana.