+ -

عن عائشة رضي الله عنها قالت: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم في مرضه الذي لم يقم منه: «لعن الله اليهود والنصارى؛ اتَّخَذُوا قُبُورَ أنبيائهم مساجد». قالت: ولولا ذلك لأُبْرِزَ قبره؛ غير أنه خُشِيَ أن يتخذ مسجدًا.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga A`isha -Allah ya kara yarda da ita- ta ce: manzon Allah -mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi- ya fada a cikin rashin lafiyar da bai tashi daga ita ba: {Allah ya tsinewa yahudu da nasara saboda sun riki kaburburan annabawansu masallatai}.ta ce: badon haka ba da an fito da kabarinsa, banda anajin tsoron a rike shi masallaci.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Allah ya aiko manzanni domin su tabbatar da tauhidi, ya kasance mafificin su shi ne annabi muhammad mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi mai kwadayi ne kan hakan, kuma mai kwadayi ne bisa toshe hanyoyin shirka, A`isha Allah ya kara yarda da ita ta kasance, ita ce tayi jiyyar annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi cikin rashin lafiyar da ya rasu a cikin ta, ita ce tana wajen a lokacin da aka karbi ransa mai girma. sai ta ambaci cewa a cikin wannan rashin lafiyar da bai tashi daga shi ba, ya ji tsoron kada a riki kabarin sa masallaci, da za`a rika yin salla a wajen sa, sai wannan halin ya bayu izuwa bautata masa koma bayan Allah madaukaki sai ya ce: ''Allah ya tsinewa yahudu da nasara saboda sun riki kaburburan annabawansu masallatai'' yana yin addu`a a kansu ko yana bada labarin cewa Allah yatsine musu, wannan yana bayyana cewar hakan ya faru ne a karshen rayuwar sa kuma ba`a shafe ba, yana tsoratarwa daga wannan aikin nasu don haka ya sanar da sahabbai Allah ya kara yadda a garesu manufar sa, sai suka sanya shi cikin dakin A`isha, kuma ba`a nakalto daga wajensu ba, ko daga wajen wadanda suka biyo bayan su daga cikin magabata, cewa su sun nufi kabarin sa madaukaki domin su shiga wajensa suyi salla kuma suyi addu`a a wajesa ba Har sai da aka zo aka canja sunna da bidi`a, aka rika daura damara don ziyarar kaburbura, sai Allah ya kiyaye annabinsa daga abinda yake ki a aikata a kabarin sa, sai ya katange shi da shamaki guda uku masu kauri, babu wata dama ga kowane dan`bidi`a da zai iya kutsawa ciki ya shiga ciki.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Portuguese
Manufofin Fassarorin