+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَيْسَ مِنَّا مَنْ لَطَمَ الخُدُودَ، وَشَقَّ الجُيُوبَ، وَدَعَا بِدَعْوَى الجَاهِلِيَّةِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1294]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1294]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani kuma ya tsoratar akan wasu ayyukan mutanen Jahiliyya, sai ya ce: Ba ya tare da mu:
Na farko: Wanda ya mari kundukuki (kumatu) an keɓanci kundukuki dan kasancewarsa shi ne galibi a hakan, inba haka ba marin sauran fuska yana shiga cikin hanin.
Na biyu: Yaga abnida ake buɗewa daga tufa dan kai ya shiga cikinsa saboda tsananin baƙin ciki.
Na uku: Yin kururuwa irin ta mutanen Jahiliyya kamar ihu da kaico da halaka da kukan mutuwa da wanin hakan.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الرومانية Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wannan narkon a cikin hadisin yana nuni akan cewa waɗannan ayyukan suna daga cikin manyan zunubai.
  2. Wajabcin haƙuri akan masifa, da haramta fushi akan ƙaddarorin Allah masu raɗaɗi, da bayyanar da hakan: Da kukan mutuwa ko aske kai ko yaga riga ko wanin hakan.
  3. Haramcin kwaikwayon Jahiliyya da al'amuransu waɗanda mai shari'antawa bai tabbatar da su ba.
  4. Babu laifi akan damuwa da hawaye, shi ba ya kore haƙuri akan hukuncin Allah - Maɗaukakin sarki -, kawai shi tausayi ne Allah Ya sanya shi a cikin zukatan makusanta da masoya.
  5. Yarda da hukuncin Allah ya wajaba akan musulmi, idan bai yarda ba to haƙuri wajibi ne a kansa.