عن بعض أزواج النبي صلى الله عليه وسلم عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ أَتَى عَرَّافًا فَسَأَلَهُ عَنْ شَيْءٍ لَمْ تُقْبَلْ لَهُ صَلَاةٌ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2230]
المزيــد ...
Daga wasu cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce:
Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2230]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan zuwa wurin mai duba -suna ne fitacce na boka, da mai taurari, mai zane a kasa da makamantansu, irin wanda yake kafa dalilin sanin gaibu ta hanyar wasu abubuwa na farko-farkon lamari- zallar tambayarsa a kan wani abu na gaibu, zai haramta masa ladan sallah na kwanaki arba’in, wannan uƙuba ce, a kan wannan laifi, kuma zunubi ne mai girma.