+ -

عن جابر رضي الله عنه:
أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: أَرَأَيْتَ إِذَا صَلَّيْتُ الصَّلَوَاتِ الْمَكْتُوبَاتِ، وَصُمْتُ رَمَضَانَ، وَأَحْلَلْتُ الْحَلَالَ، وَحَرَّمْتُ الْحَرَامَ، وَلَمْ أَزِدْ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا، أَأَدْخُلُ الْجَنَّةَ؟ قَالَ: «نَعَمْ»، قَالَ: وَاللهِ لَا أَزِيدُ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا.

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 15]
المزيــد ...

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi -:
Lallai wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban kara komai akan hakan ba, zan shiga Aljanna? Ya ce : "Eh", ya ce: Na rantse da Allah ba zan kara komai ba akan hakan ba.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 15]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya sallaci salloli biyar, wadanda suka wajabta bai kara komai akan su ba na nafilifili, kuma ya azimci watan Ramadan bai yi tadawwa’i ba, ya kudirce halatta halal ya kuma aikata shi, ya kudirce haramta haram ya kuma nisanci ta, to shi zai shiga Aljanna.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadayin musulmi akan aikata farillai da barin abubuwan da aka haramta, da kuma manufarsa ta zama shiga Aljanna.
  2. Muhimmancin aikata halal da kudirce halaccinsa, da kuma haramta haram da kudirce haramcinta.
  3. Aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, sababi ne na shiga Aljanna.