عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«بَادِرُوا بِالْأَعْمَالِ فِتَنًا كَقِطَعِ اللَّيْلِ الْمُظْلِمِ، يُصْبِحُ الرَّجُلُ مُؤْمِنًا وَيُمْسِي كَافِرًا، أَوْ يُمْسِي مُؤْمِنًا وَيُصْبِحُ كَافِرًا، يَبِيعُ دِينَهُ بِعَرَضٍ مِنَ الدُّنْيَا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 118]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu, mutum zai wayi gari yana mumini ya kai yammaci yana kafiri, ko ya yammanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai sayar da addininsa da wata haja ta duniya".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 118]
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da mumini akan gaggawa da yawaita ayyuka na gari kafin wuyatarsu da shagaltuwa daga gare su da zuwan fitinu da shubuhohin da zasu hana aikata su, kuma zasu toshe su, masu duhu ne kamar yankin dare, yana cakuɗe gaskiya da ƙarya a cikinsu, sai banbancewa tsakaninsu ta yi wuya a wurin mutane, saboda tsananinsu mutum zai dinga kaikawo har cewa shi zai wayi gari yana mumini ya yanmanta yana kafiri, kuma ya yanmanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai bar addininsa da wani ɗan jin daɗi na duniya mai gushewa.