عَنِ الْبَرَاءِ رضي الله عنه:
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ فِي الْأَنْصَارِ: «لَا يُحِبُّهُمْ إِلَّا مُؤْمِنٌ، وَلَا يُبْغِضُهُمْ إِلَّا مُنَافِقٌ، مَنْ أَحَبَّهُمْ أَحَبَّهُ اللهُ وَمَنْ أَبْغَضَهُمْ أَبْغَضَهُ اللهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 75]
المزيــد ...
Daga Al-Barra - Allah Ya yarda da shi -:
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi cewa shi ya fada a sha'anin mutane Madina: "Ba mai sonsu sai mumini, kuma babu mai kinsu sai munafiki, wanda ya so su Allah zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 75]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa son mutanen Ansar daga mutanen Madina, alama ce akan cikar imani; wannan dan rigayarsu a taimakon Musulunci da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kokari akan tarbar musulmai, da bada dukiyoyinsu da rayukansu a tafarkin Allah, kuma cewa kinsu alama ce ta munafunci. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa wanda ya so mutanen Madina Allah Zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi.