عَن زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ جَهَّزَ غَازِيًا فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَقَدْ غَزَا، وَمَنْ خَلَفَ غَازِيًا فِي سَبِيلِ اللَّهِ بِخَيْرٍ فَقَدْ غَزَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2843]
المزيــد ...
Daga Zaid ɗan Khalid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2843]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya tanadarwa wani mayaki a tafarkin Allah sabubban tafiyarsa da abinda yake bukatuwa gare shi daga abinda babu makawa gare shi na makami da abin hawa, da abinci, da ciyarwa da waninsu; to shi yana cikin hukuncin mai yin yaki, kuma ladan mayaki zai same shi .
wanda ya jibinci al'amarin mayaki da alheri, kuma ya maye gurbinsa a cikin kula da iyalansa a lokacin da ba ya nan to shi yana cikin hukuncin mayaki yake.