+ -

عَن سَهْلِ بْنِ حُنَيْفٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ سَأَلَ اللهَ الشَّهَادَةَ بِصِدْقٍ بَلَّغَهُ اللهُ مَنَازِلَ الشُّهَدَاءِ، وَإِنْ مَاتَ عَلَى فِرَاشِهِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1909]
المزيــد ...

Daga Sahl ɗan Hunaif - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah Zai kai shi matsayin shahidai, koda ya mutu akan shinfiɗarsa".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1909]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya nemi shahada da mutuwa a tafarkin Allah, kuma ya kasance mai gaskiya mai tsarkake niyyarsa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, Allah Zai ba shi darajojin shahidai saboda niyyarsa ta gaskiya koda ya mutu akan shinfiɗa ba a yaki ba.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Gaskiyar niyya tare da aikata abin da za'a iya, sababi ne na samun abin nufi na lada da sakamako, koda bai yi aikin da ake nema ba.
  2. Kwaɗaitarwa akan jihadi da neman shahada a tafarkin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
  3. Baiwar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan al'ummar, shi (Allah) yana bada mafi ɗaukakar darajoji a cikin aljanna da kankanin aiki.