عَنِ ابْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«سَتَكُونُ أَثَرَةٌ وَأُمُورٌ تُنْكِرُونَهَا» قَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ فَمَا تَأْمُرُنَا؟ قَالَ: «تُؤَدُّونَ الحَقَّ الَّذِي عَلَيْكُمْ، وَتَسْأَلُونَ اللَّهَ الَّذِي لَكُمْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3603]
المزيــد ...
Daga Dan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Za'a samu babakere da wasu al'amuran da zaku kisu" suka ce : Ya Manzon Allah mezaka umarcemu? Ya ce: "Ku bada hakkin da ya wajaba akanku, kuma ku roki Allah hakkinku ".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3603]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shugabanni zasu shugabanci musulmai, za su yi babakere da dukiyoyin musulmai da wasunsu daga al'amuran duniya, za su dinga juyasu kamar yadda suke so zasu hana musulmai hakkokinsu a dukiyar . Kuma wasu al'amuran da za'aki a Addini zasu kasance daga garesu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka yi tambaya: Me za su aikata a wannan halin? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ba su labarin cewa kada wawure (dukiya da suka yi) ya hanaku abinda ya wajaba akanku daura da su na ji da bi, kai ku yi hakuri ku ji ku bi , kada ku yi jayayya da su a al'amari, kuma ku roki Allah hakin dake gareku, kuma Ya gyrasu ya tunkude sharrinsu da zalincinsu.