عن عَبْد الرَّحْمَنِ بْن سَمُرَةَ رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال له: «يا عبد الرحمن بن سَمُرَة، لا تَسْأَلِ الإِمَارَةَ؛ فإنك إن أُعْطِيتَها عن مَسْأَلَةٍ وُكِلْتَ إليها، وإن أُعْطِيتَهَا عن غير مَسْأَلَةٍ أُعِنْتَ عليها، وإذا حَلَفْتَ على يمينٍ فرأيتَ غيرها خيرًا منها، فَكَفِّرْ عن يمينك، وَأْتِ الذي هو خير».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdurrahman Dan samra yana cewa cewa Annabi ya ce masa: "Ya kai Abdurraahman Dan Samra, kada ka kuskura ka nemi Mulki, cewa in aka baka shi sabida ka nema sai a barka da kanaka, kuma in aka baka bakai ka nema ba sai Allah ya taimakeka akansa, kuma idan kayi rantsuwa akan wani abu sai kaga wani mafi alkairi daga rantsuwar, to kayi kaffarar rantsuwarka, kuma kayi abinda yafi Alkairin"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi ya hana tambayar Mulki; domin duk wanda ya nema kuma aka bashi to sai ya tozarta kuma sai anbarshi da kwadayinsa a cikin Duniya kuma sai ya fifita Mulkin akan lahirarsa, kuma idan aka bashi mulikin bashi ya nema ba to Allah zai taimake shi akai, kuma cewa rantsuwa akan wani abu bata hana yin Alkairi, sabida idan wanda ya rantse yaga wani Alkairin da yafi rantsuwarsa to sai ya warware rantsuwar tasa da kaffara, sannan ya aikata Alkairinsa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin