+ -

عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم «نهى عن لُبُوسِ الحَرِيرِ إلا هكذا، ورَفَعَ لنا رسول الله صلى الله عليه وسلم أُصْبُعَيْهِ: السَّبَّابَةَ، والوُسْطَى». ولمسلم «نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم عن لُبْس ِالحَرِيرِ إلا مَوْضِعَ أُصْبُعَيْنِ، أو ثلاثٍ، أو أربعٍ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah- " ya hana sanya Alhariri sai dai haka, sai ya daga mana yatsunsa biyu: Manuniya da y'ar tsakkiya". A wata ruwayar Muslim "ya Manzon Allah tsira da amincin Allah Manzon Allah ya hana sanya alhariri sai a gurin yatsu biyu, ko uku, ko hudu."
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah ya hana maza sanya alhariri sai dai a inda aka kebance, watau y'an yatsu biyu da aka ambata cikin hadisin Buhari da Muslim da ya gabata da kuma ruwayar Muslim da ta kara da cewa: ko uku ko hudu, don haka sai a yi amfani da mafi yawa, shi ne gwargwadon yatsu hudu ba laifi. ka duba Littafin Taasisil'Ahkam

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin