+ -

عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم -: «إنّي والله -إنْ شاء الله- لا أَحلف على يمين، فأرى غيرها خيراً منها إلاَّ أَتيتُ الَّذِي هو خير، وتحلَّلْتُهَا».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

An karbo daga abi musa al-ash`ariy- Allah ya kara yarda a gareshi- abin daukakawa zuwa ga annabi: { Lallai ni na rantse da Allah - da yardar Allah- bana yin wata rantsuwa bisa aikata wani abu da nayi rantsuwa akai, sai naga waninsa ya fi alheri da na aikata shi face na zo da wanda shi yafi alheri, sai na warware ta }.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Lallai annabi- mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi- ya bada labari gameda kansa cewa idan yayi rantsuwa bisa aikata wani abu sa`annan daga baya yaga cewa lallai alherin yana cikin rashin cigaba da aikata wannan abun da yayi rantsuwa akai sai ya barta da barin abinda yayi rantsuwa akansa sai yayi kaffarar ita wannan rantsuwar sai ya lizimci wannan abin da yafi alheri daga aikata shi ko barin shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili
Manufofin Fassarorin