عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَوَّلُ مَا يُقْضَى بَيْنَ النَّاسِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِي الدِّمَاءِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1678]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1678]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa farkon abinda za’a yi hukunci a tsakanin mutane a zalincin junansu a ranar Alkiyama: A jinane ne, kamar kisa da raunuka.