kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

"Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa".
عربي Turanci urdu
Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "@Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa*, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".
عربي Turanci urdu
"Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".
عربي Turanci urdu
"Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da Allah zai kuɓutar da shi, shin ba zan baku labarin 'yan wuta ba? duk mai ƙaton ciki mai kaushin rai mai girman kai".
عربي Turanci urdu
Akwai matakai guda dari a Sama wanda Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa
عربي Turanci urdu
‘’Haqiqa za’a zo da wani mutum mai girma mai qiba ranar tashin Alqiyama amma a wajen Allah ba za’a gwada shi ba ma da fiffiken Sauro ‘’
عربي Turanci urdu
"Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".
عربي Turanci urdu
Wasu daga cikinsu suna dauke wuta a kan dugadugansa, wasu kuma suna dauke shi zuwa gwiwowinsa, wasu kuma suna daukarsa
عربي Turanci urdu
"Lallai Allah -Maigirma da Daukaka- zai ce Ranar Al-kiyama ya kai Dan Adam nayi rashin lafiya amma baka dubani ba"
عربي Turanci urdu
"Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)?* suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dirhami ko kaya, sai ya ce: "Lallai cewa muflis daga al'ummata zai zo ranar alƙiyama da sallah da azumi da zakka, zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, kuma ya yi wa wannan ƙazafi, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya daki wannan, sai a bawa wannan daga kyawawan ayyukansa, wannan ma daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukansa sun ƙare kafin a biya abin ke kansa sai a ɗauka daga kurakuransa sai a watsa masa, sannan a watsa shi a cikin wuta".
عربي Turanci urdu
"Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta*, sai a ƙona shi a kansu a cikin wutar Jahannama, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas, duk lokacin da suka ƙone sai a dawo da su, a cikin wani yinin da gawargwadansa shekara dubu hamsin ne, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai yaga hanyarsa, ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta".
عربي Turanci urdu
Ubangiji na yayi mun Al-qawari shigar da Al-umma ta Dubu Saba'in ba tare da Hisabi, kuma babu Azaba kuma kowace Dubu Saba'in wata Dubun da Kyauta Uku da kyaututtukan Ubangiji na
عربي Turanci urdu
Ubangijinmu zai yaye Maqyagyamarsa, sai kowane Mumini yayi sujada a gare shi Mace da Namiji, sai Waxanda suka kasance suna Sujada a Duniya saboda riya da jiyarwa su tsaya, sai su tafi suyi Sujada sai bayansu ya Sandare baki xaya
عربي Turanci urdu
Ya Manzon Allah, Shin zamu ga Ubangijinmu ? ya ce: Shin kuna iya ganin Rana? da Wata idan gari yai wasai?
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira*. Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Yayin da (aya) ta sauka @{Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima}* [Al-Takasur: 8], sai Zubair ya ce: Ya Manzon Allah, shin wace ni'ima ce za a tambayemu game da ita, bakake biyu ba ne kaɗai; dabino da ruwa? sai ya ce: "lallai dai kam daa sannu zai kasance".
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya haxiye fushi, kuma yana da ikon ya ya rama, Allah zai kirawo shi a cikin Mutane a Ranar Al-qiyama ya zava Masa daga cikin Matan Hurul-Aini abunda ya so
عربي Turanci urdu
Lallai, Allah madaukaki yana cewa a ranar kiyama: Ina wadanda suke kauna a cikin Mai girma na? A yau zan yi musu inuwa a cikin inuwa ta, rana babu wata inuwa sai tawa.
عربي Turanci urdu
"Allah Mai xaukaki zai naxe sammai da a ranar Al-qiyama sannan ya xaukesu da Hannunsa na Dama sannan ya ce: Ni ne Mai Mulki ina masu jabberanci? kuma sannan sai naxe qasa ma da Hannunsa na Hagu sannan ya ce: Ni ne Mai Mulki ina masu jabberanci?"
عربي Turanci urdu
Allah mai girma da daukaka ya ce: Wadanda suke kauna a cikin Jalali suna da mimbarin haske wanda annabawa da shahidai suka raya shi.
عربي Turanci urdu
«‌Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami*, idan yana da wani aiki na gari za'a ɗauka daga cikin shi gwargwadan zalincinsa, idan ba shi da wasu kyawawan ayyuka za'a ɗauka daga munanan ayyukan ɗan'uwansa (da ya zalinta) sai a jibga masa su».
عربي Turanci urdu
«‌Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya»*. Na ce: Ya Manzon Allah! mata da maza baki ɗaya sashinsu yana kallon sashi? Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «‌Ya A'isha, al'amarin ya fi tsanani a ce sashinsu yana kallon sashi».
عربي Turanci urdu
Mutane suna tsayuwa ne zuwa ga Ubangijin talikai har sai dayansu ya kasance ba ya cikin zabensa zuwa rabin kunnuwansa
عربي Turanci urdu
Lallai ne ku bada zuwa Ma'abotansa Ranar Al-kiyama har sai anyi sakamako ga Akuya Mai kaho da Mara Kaho
عربي Turanci urdu
Saihan da Jihan da Furat da Nil baki xayan su kogunan Al-janna ne
عربي Turanci urdu
Wuta da Aljanna sunyi Jayayya, sai wuta ta ce: an zaveni saboda masu girman kai, da Masu jiji da Kai, kuma Aljanna ta ce: Ni kuma babu mai shiga ta sai raunanan Mutane da waxanda ba komai ba, da wacanda idonsu bai buxe da Duniya ba
عربي Turanci urdu
Za'a tashi Mutane Ranar Al-qiyama -ko kuma ya ce Bayi= tsirara basu da Kaciya
عربي Turanci urdu
Lallai kafiri idan ya aikata Kyakkyawan aiki, sai a ciyar da shi Abinci a Duniya, Kuma Mumini Saboda Allah yana masa tanadin Kyawawan lada a Lahira, kuma ya bibiye shi da arziki a cikin Duniya kan biyayyarsa
عربي Turanci urdu
"Ladanai sune mafiya tsawon wuyaye a ranar alƙiyama".
عربي Turanci urdu
Idam Ranar Al-kiyama ta Kasance Allah ai Tura ga kowane Musuli Bayahude daya Ko banasare, sai yace wannan zai kwanceka daga Wuta
عربي Turanci urdu
Ku karanta Alqurani domin zai zo Ranar Alkiyama mai ceton Ma'abotansa
عربي Turanci urdu
«Za'a kusantowa halitta da rana a yinin Alƙiyama har sai ta kusa kamar gwargwadan mil daga gare su»*, Sulaim ɗan Amir ya ce: Na rantse da Allah ban san me yake nufi da mil ba? Shin faɗin ƙasa ne, ko kuma mil ɗin da ake wa ido kwalli da shi? - ya ce: «Sai mutane su zama akan gwargwadan ayyukansu cikin gumi, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa idanun sawunsa, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa guwoyinsa, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa kwankwasonsa, daga cikinsu akwai wanda zai yi masa linzmi linzami» ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi nuni da hannunsa zuwa bakinsa.
عربي Turanci urdu
«Lallai mafi ƙankantar matsayin ɗayanku a cikin aljanna shi ne Ya ce masa: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, sai Ya ce da shi: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce da shi: @Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi».
عربي Turanci urdu
"Ni ne shugaban mutane a ranar alƙiyama, shin kun san daga menene hakan? @Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba*, sai mutane su ce: Shin bakwa ganin abinda haƙiƙa ya kai muku ? shin bakwa duba wanda zai yi muku ceto zuwa ga Ubangijinku ba? sai wasu daga mutane su ce wa wasu: Ku je gurin (annabi) Adam, sai su zo wa Adam - aminci ya tabbata agare shi - sai su ce masa: Kai ne uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya busa maka daga ranSa, kuma Ya umarci mala'iku sai suka yi maka sujjada, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana? sai Adam ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushi a yau bai taba irin wannan fushin ba, kuma ba zai taba yin irin wannan fushin ba, kuma lallai ni hakika Ya hanani daga bishiya sai na saba maSa, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Nuhu. Sai su zo wa (annabi) Nuhu sai su ce: kai Nuhu, lallai kai ne farkon manzanni zuwa mutanen kasa, hakika Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana, shin baka nema mana ceto ga Ubangijinka ba? sai ya ce: Lallai Ubangijina Ya yi fushi a yau bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba, kuma lallai cewa ni akwai mummunar addu'ar da na yi akan mutanena, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi gurin (annabi) Ibrahim. Sai su zo wa (annabi) Ibrahim sai su ce: kai Ibrahim, kai ne Annabin Allah kuma badaɗayinSa daga mutanen ƙasa, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce musu: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba irinsa, lallai cewa ni na yi ƙarya sau uku, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga (annabi) Musa. Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai Musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijnka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai ni naa kashe wani rai da ba'a yi umarni da in kasheta ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Isa. Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: kai Isa, kaine Manzon Allah kuma kalmarSa da ya jefata zuwa Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfidar goyo, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai Isa ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, ba zai anbaci wani zunubi ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -". Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce kai ne Manzon Allah kuma cika makin Annabawa, hakika Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai in tafi, sai in zo ƙarƙashin al’arshi sai infaɗi ina mai sujjada ga Ubangina, sannan Allah Ya buɗe mini daga godiyarSa da kyakkyawan yabo gareShi na wani abinda bai taɓa buɗewa wani a gabani na ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka shi, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in dago kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Uabngiji, sai ace: Ya Muhammad ka shigar daga al'ummarka wadanda babu wani hisabi akansu ta kofar dama daga kofofin aljanna, kuma su suna tarayya da mutane a koma bayan haka na kofofi". sannan ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lalai tsakanin ginshikai biyu daga ginshikan aljanna kamar tsakanin Makka ne da Hajar, ko tsakanin Makka ne da Busra".
عربي Turanci urdu
«Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske*, ba sa fitsari ba sa bahaya, ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abin taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski, kuma abin kunna tiraren wutarsu shi ne icen tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inun (Masu tsananin farin ido da tsananin ƙwayar baƙin da ke cikin idon), suna a kan halittar mutum ɗaya, akan surar babansu (Annabi) Adam, zira'i sittin a cikin sama».
عربي Turanci Indonisiyanci
«Akwai darajoji ɗari a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja kamar tsakanin sama da ƙasa ne, Firdausi it ce mafi ƙololuwarsu (a daraja), kuma daga nanne ƙoramun aljanna suke ɓuɓɓugowa, kuma a samanta ne Al’arshi yake. @Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi».
عربي Turanci Indonisiyanci