Karkasawa: Aqida . Imani da Ranar Lahira .
+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ أَوَّلَ زُمْرَةٍ يَدْخُلُونَ الجَنَّةَ عَلَى صُورَةِ القَمَرِ لَيْلَةَ البَدْرِ، ثُمَّ الَّذِينَ يَلُونَهُمْ عَلَى أَشَدِّ كَوْكَبٍ دُرِّيٍّ فِي السَّمَاءِ إِضَاءَةً، لاَ يَبُولُونَ وَلاَ يَتَغَوَّطُونَ، وَلاَ يَتْفِلُونَ وَلاَ يَمْتَخِطُونَ، أَمْشَاطُهُمُ الذَّهَبُ، وَرَشْحُهُمُ المِسْكُ، وَمَجَامِرُهُمْ الأَلُوَّةُ الأَنْجُوجُ، عُودُ الطِّيبِ وَأَزْوَاجُهُمُ الحُورُ العِينُ، عَلَى خَلْقِ رَجُلٍ وَاحِدٍ، عَلَى صُورَةِ أَبِيهِمْ آدَمَ، سِتُّونَ ذِرَاعًا فِي السَّمَاءِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3327]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske, ba sa fitsari ba sa bahaya, ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abin taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski, kuma abin kunna tiraren wutarsu shi ne icen tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inun (Masu tsananin farin ido da tsananin ƙwayar baƙin da ke cikin idon), suna a kan halittar mutum ɗaya, akan surar babansu (Annabi) Adam, zira'i sittin a cikin sama».

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3327]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin farkon jama'a ta muminai waɗanda zasu shiga aljanna fuskokinsu suna kan surar wata daren goma sha huɗu a haske, sannan masu biye musu suna kan surar tauraro mafi tsananin haske, kuma suna da wasu siffofin cika inda ba sa fitsari ba sa bahaya, kuma ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abubuwan taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski. Kuma abin kunna tiraren wutarsu yana tada ƙanshi mafi daɗin ƙanshin tirare kuma mafi ƙanshin tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inu, halittarsu akan halittar mutum ɗaya ne akan surar babansu Annabi Adam a tsawo da kuma halitta; tsawon jikinsa zira'i sittin ne a sama.

Fassara: Indonisiyanci Vietnam Swahili Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin siffar 'yan aljanna, kuma cewa su suna da fifiko a cikinta gwargwadan darajojinsu da kuma ayyukansu.
  2. Anafni da tashbihi (karantawa) don kusanto da ma'anoni da kuma sharhinsu.
  3. AlƘurɗubi ya ce: Za'a iya cewa to wace buƙata suke da ita na taje kai alhali su matasa ne kuma gashinsu ba ya datti? Kuma wace buƙata ce da su ga tiraren wuta alhali ƙanshinsu ya fi almiski? Ya ce: Za'a amsa da cewa ni'imar 'yan aljanna na ci da sha da tufafi da tirare badan jin raɗaɗin yunwa ba ne ko ƙishirwa ko tsiraici ko wari, kawai su daɗi ne a jere da ni'imomi a jere, kuma hikima a cikin hakan cewa su suna ni'imtuwa da nau'in abinda suka kasance suna ni'imtuwa da shi ne a duniya.