عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ أَنْظَرَ مُعْسِرًا، أَوْ وَضَعَ لَهُ، أَظَلَّهُ اللهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تَحْتَ ظِلِّ عَرْشِهِ يَوْمَ لَا ظِلَّ إِلَّا ظِلُّهُ».
[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 1306]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 1306]
Annabi - tsira da amincin Allah - su tabbata agare shi - ya ba da labari cewa wanda ya saurarawa wanda ake bi bashi, ko ya sarayar masa daga bashinsa, to, sakamakonsa: shi ne Allah Zai inuwantar da shi ƙarƙashin al-Arshinsa a ranar Alƙiyama, wanda rana zata kusanto kawunan bayi a cikinta, kuma zafinta zai tsananta akansu. Babu wanda zai samu wata inuwa sai wanda Allah Ya inuwantar da shi.