lis din Hadisai

"Lallai cewa yana daga mafi sharrin mutane wadanda alkiyama zata riske su alhali suna raye, da wanda yake rikon kaburbura masallatai".
عربي Turanci urdu
"Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kalmarSa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare Shi, kuma aljanna gaskiya ce haka wuta ma gaskiya ce, @Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa".
عربي Turanci urdu
"Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa".
عربي Turanci urdu
Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "@Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa*, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama*, sai Ya bude masa fayil dinsa x asa'in da tara, kowanne fayil tamkar iya ganinka ne, sannan Ya ce: Shin kana musun wani abu daga wannan? Shin marubutaNa masu kiyayewa sun zalinceka ne? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai Ya ce: Shin kana da wani hanzari? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai (Ubangiji) Ya ce: Eh, lallai kanada wani abu kyakkyawa a wurinmu, a yau babu wani zalinci akanka, sai a fitar da wani kati a cikinsa akwai: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, sai ya ce: ka zo wajan ma'aninka, sai ya ce; ya Ubangiji wannan wanne katine tare da wadannan fayilillikan? Sai Ya ce; Lallai cewa kai ba za’a zalinceka ba, sai ya ce: Sai a dora fayilillikan a bangaren ma'auni , katin kuma a daya ma'aunin, sai fayililliakn su yi sauki, kuma katin ya yi nauyi, wani abu ba zai yi nauyi tare da sunan Allah ba".
عربي Turanci urdu
"Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi* - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta . Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".
عربي Turanci urdu
"Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".
عربي Turanci urdu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "@Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci*" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
عربي Turanci urdu
: :
عربي Turanci urdu
"Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta,* wacce zai ce ita ce aljanna to ita ce wuta, lallai ni ina gargaɗarku kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗi al'ummarsa da shi".
عربي Turanci urdu
"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan"* sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".
عربي Turanci urdu
Daga kanka ka fada za'a ji, ka roka a baka, ka nemi ceto za'a baka ceton
عربي Turanci urdu
"Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da Allah zai kuɓutar da shi, shin ba zan baku labarin 'yan wuta ba? duk mai ƙaton ciki mai kaushin rai mai girman kai".
عربي Turanci urdu
Akwai matakai guda dari a Sama wanda Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa
عربي Turanci urdu
‘’Haqiqa za’a zo da wani mutum mai girma mai qiba ranar tashin Alqiyama amma a wajen Allah ba za’a gwada shi ba ma da fiffiken Sauro ‘’
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - har sai ya sanya kiyayewarSa, sai Ya tabbatar masa da zunubansa*, sai Ya ce: Shin kana sane ? sai ya ce: Eh ya Ubangiji ina sani, ya ce: Lallai cewa Ni haƙiƙa Na suturtasu gareka a duniya, kuma cewa lallai Ni Zan gafarta maka su a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa, amma kafirai da munafukai, sai a kirasu akan kawunan halittu waɗannan sune waɗanda suka yi wa Allah ƙarya".
عربي Turanci urdu
"Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya yi mubaya'a ga limami kuma ya ba shi cinikin hannunsa da 'ya'yan zuciyarsa, to ya rantse da shi idan zai iya.
عربي Turanci urdu
Wasu daga cikinsu suna dauke wuta a kan dugadugansa, wasu kuma suna dauke shi zuwa gwiwowinsa, wasu kuma suna daukarsa
عربي Turanci urdu
Kowane bawa za a tayar da shi ranar tashin kiyama a cikin yanayin da ya mutu a kansa
عربي Turanci urdu
"Lallai Allah -Maigirma da Daukaka- zai ce Ranar Al-kiyama ya kai Dan Adam nayi rashin lafiya amma baka dubani ba"
عربي Turanci urdu
"Babu wani annabi fa sai ya gargadi Mutanensa Mai Ido daya Makaryaci
عربي Turanci urdu
"Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)?* suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dirhami ko kaya, sai ya ce: "Lallai cewa muflis daga al'ummata zai zo ranar alƙiyama da sallah da azumi da zakka, zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, kuma ya yi wa wannan ƙazafi, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya daki wannan, sai a bawa wannan daga kyawawan ayyukansa, wannan ma daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukansa sun ƙare kafin a biya abin ke kansa sai a ɗauka daga kurakuransa sai a watsa masa, sannan a watsa shi a cikin wuta".
عربي Turanci urdu
"Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta*, sai a ƙona shi a kansu a cikin wutar Jahannama, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas, duk lokacin da suka ƙone sai a dawo da su, a cikin wani yinin da gawargwadansa shekara dubu hamsin ne, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai yaga hanyarsa, ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta".
عربي Turanci urdu
Ubangiji na yayi mun Al-qawari shigar da Al-umma ta Dubu Saba'in ba tare da Hisabi, kuma babu Azaba kuma kowace Dubu Saba'in wata Dubun da Kyauta Uku da kyaututtukan Ubangiji na
عربي Turanci urdu
Ubangijinmu zai yaye Maqyagyamarsa, sai kowane Mumini yayi sujada a gare shi Mace da Namiji, sai Waxanda suka kasance suna Sujada a Duniya saboda riya da jiyarwa su tsaya, sai su tafi suyi Sujada sai bayansu ya Sandare baki xaya
عربي Turanci urdu
Ya Manzon Allah, Shin zamu ga Ubangijinmu ? ya ce: Shin kuna iya ganin Rana? da Wata idan gari yai wasai?
عربي Turanci urdu
A iyakokin Madina Mala'iku Annoba da Dujal basa shigar ta
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu
عربي Turanci urdu
"Lallai cewa idan ɗayanku ya mutu za’a bijiro masa da mazauninsa safiya da maraice*, idan ya kasance daga cikin 'yan aljanna ne to yana daga cikin 'yan aljanna, idan ya kasance daga cikin 'yan wuta to yana daga cikin 'yan wuta, sai a ce: Wannan mazauninka ne har sai Allah Ya tasheka ranar alƙiyama".
عربي Turanci urdu
"Lallai wannan al'amarin zai kai inda dare da rana suka kai, kuma Allah ba Zai bar wani gidan bulo ko na gashi ba sai Allah Ya shigar da wannan addinin cikinsa*, da girman mai girma ko da ƙasƙancin kaskantacce, buwaya ce da Allah Yake ɗaukaka musulunci da ita, da ƙasƙancin da Allah Yake ƙasƙantar da kafirci da shi"* Tamimi al-Dari ya kasance yana cewa: Haƙiƙa na san hakan a iyalan gidana, haƙiƙa wanda ya musulunta a cikinsu alheri da ɗaukaka da buwaya ya same shi, wanda yake kafiri a cikinsu kuma ƙasƙanci da wulaƙanci da jiziya sun same shi .
عربي Turanci urdu
"Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira*. Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".
عربي Turanci urdu
"Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, Ibnu Maryam (Annabi Isa) ya kusa ya sauka a cikinku yana mai hukunci mai adalci, sai ya karya gicciyayye (cross), ya kashe alade, ya sarayar da jizya, dukiya ta yawaita har babu wanda zai karbeta".
عربي Turanci urdu
"Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka ganta sai su yi imani gaba dayansu*, wannan yayin da: {Wani rai imanin sa ba zai anfane shi ba, bai yi imani ba kafin nan, ko bai aikata alheri a imanin na sa ba} [Al-An'am: 158] kuma lalli Alkiyama za ta tsaya alhali mutum biyu za su shinfida tufafinsu a tsakaninsu ba za su saida shi ba, ba kuma za su ninkeshi ba, lallai Alkiyama za ta tsaya alhali hakika mutum ya juya da nonon taguwarsa da ta tatsa ba zai dandane shi ba, lallai Alkiyama za ta tsaya alhali shi yana yabe tafkinsa ba zai shayar a cikinsa ba, Alkiyama za ta tsaya alhali hakika dayanku ya daga lomarsa zuwa bakinsa ba zai cinyeta ba".
عربي Turanci urdu
"Alkiyama ba zata tsaya ba har sai zamani ya kusantowa juna*, sai shekara ta zama kamar wata, wata kuma ya zama kamar Juma'a (sati guda), Juma'a kuma ta zama kamar yini, yini ya zama kamar awa, awa kuma ta zama kamar konewar ganyen dabino".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi*, kofunansa kamar taurarin sama ne, wanda ya sha daga gare shi ba zai yi kishirwa ba har abada".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Na ce: Ya Manzon Allah menene kofunan tafki? (Sai) ya ce: "@Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, kofunansa sun fi yawan adadin taurarin sama* ku saurara a cikin duhun daren da babu hazo, kofunan Aljanna wanda ya sha daga garesu ba zai yi kishirwa ba har karshen al’amarinsa (na kishirwa), indararo biyu ne suke zuba a cikinsa daga Aljanna, wanda ya sha daga gareshi Ba zai yi kishirwa ba, fadinsa tamkar tsawonsa ne, tsakanin Amman zuwa Ailata, ruwansa ya fi nono tsananin fari, kuma ya fi zuma zaki".
عربي Turanci urdu
"Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki*, sai mai kira ya yi kira: Yaku 'yan Aljanna, sai su dago kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, dukkaninsu kuma sun ganta, sannan ya yi kira: Yaku 'yan wuta, sai su miko kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu sun ganta, sai a yankata sannan ya ce: Ya ku 'yan Aljanna dawwama babu mutuwa, ya ku 'yan wuta dawwama babu mutuwa, sannan ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadin ranar nadama yayin da aka hukunta al'amari alhali su suna cikin rafkana} [Maryam: 39], wadannan suna cikin rafkanannun mutane a duniya {Su ba su Imani ba} [Maryam: 39]".
عربي Turanci urdu
"Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama*", (Sai) aka ce: Ya Manzon Allah, ta kasance ta isa (dan azabtarwa), ya ce: "An fifita ta a kansu da yanki sittin da tara, kowannen su tamkar zafinta yake”.
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Cewa wani mutum ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah ! ina da bayi biyu suna yi mini karya suna ha'intata suna saba mini, ni kuma ina zaginsu ina dukansu, ya matsayina yake garesu (a urin Allah?) Ya ce: "@Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu*, idan ukubar da ka yi musu gwargwadan laifinsu ne, ya zama daidai wa daida, babu komai gareka ko akanka. Idan ukubar ka akansu kasa da laifin su ne to ya zama falala gareka, idan ukubarka garesu sama da laifin su ne za’a yi masu sakayyar karin daga gareka", ya ce: Sai mutumin yadan yi nesa sai ya fara kuka yana kururuwa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ba ka karanta littafin Allah ba: {zamu sanya ma'auni na adalci ga yinin Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abu ba}. karanta zuwa karshenta, sai mutumin ya ce; Wallahi ya Manzon Allah, ban ji wani abu gareni dasu ba mafi alheri daga rabuwa da su, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne gaba dayansu.
عربي Turanci urdu
Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya zantar damu cewa wani mutum ya ce: Ya Annabin Allah ya za’a tashi kafiri akan fuskarsa? Ya ce: "@ Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?*"Katada ya ce: Eh na rantse da buwayar Ubangijinmu.
عربي Turanci urdu
Yayin da (aya) ta sauka @{Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima}* [Al-Takasur: 8], sai Zubair ya ce: Ya Manzon Allah, shin wace ni'ima ce za a tambayemu game da ita, bakake biyu ba ne kaɗai; dabino da ruwa? sai ya ce: "lallai dai kam daa sannu zai kasance".
عربي Turanci urdu
"Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su"
عربي Turanci urdu
"Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati*, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".
عربي Turanci urdu
Namiji yana bacci yana bacci, kuma an kwace amanar daga zuciyarsa, don haka alamarta ta kasance kamar laka, to sai ya yi barci, kuma amintar da ita ta kasance daga zuciyarsa, don haka tasirinsa ya kasance kamar alamar magul
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to bakonsa ya girmama ladar sa. ”Suka ce:“ Mene ne sakamakonsa? Ya Manzon Allah, ya ce: Yininsa da darensa, da karimcinsa kwana uku ne, don haka abin da ya kasance a baya sadaka ce a gare shi
عربي Turanci urdu
Wanda raina yake a hannunsa duniya ba ta tafiya har sai wani mutum ya tsallake kabari, sai ya yi birgima a kansa ya ce: Ina ma dai in kasance wurin mai wannan kabarin, kuma babu addini a ciki. Bala'i kawai
عربي Turanci urdu
Sa'a ba za ta tashi ba har sai Yufiretis ta janye daga dutsen zinariya don yaƙi da ita, kuma ana kashe kowane ɗari da tasa'in da tara.
عربي Turanci urdu
Sun bar garin kamar yadda yake, ba abin da ya rufe su sai makoki
عربي Turanci urdu
Bari a samu lokaci ga mutanen da wani mutum zai yi dawafin sadaka ta zinariya kuma ya ga ba wanda zai karba daga gare shi, kuma an ga mutum daya yana bin mata arba'in suna biye da shi.
عربي Turanci urdu
Masu adalci na farko sun tafi na farkon, kuma tabo ya kasance kamar sha’ir ko dabino
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya haxiye fushi, kuma yana da ikon ya ya rama, Allah zai kirawo shi a cikin Mutane a Ranar Al-qiyama ya zava Masa daga cikin Matan Hurul-Aini abunda ya so
عربي Turanci urdu
Lallai, Allah madaukaki yana cewa a ranar kiyama: Ina wadanda suke kauna a cikin Mai girma na? A yau zan yi musu inuwa a cikin inuwa ta, rana babu wata inuwa sai tawa.
عربي Turanci urdu
"Allah Mai xaukaki zai naxe sammai da a ranar Al-qiyama sannan ya xaukesu da Hannunsa na Dama sannan ya ce: Ni ne Mai Mulki ina masu jabberanci? kuma sannan sai naxe qasa ma da Hannunsa na Hagu sannan ya ce: Ni ne Mai Mulki ina masu jabberanci?"
عربي Turanci urdu
Allah mai girma da daukaka ya ce: Wadanda suke kauna a cikin Jalali suna da mimbarin haske wanda annabawa da shahidai suka raya shi.
عربي Turanci urdu
Na farkonsu da na karshensu za a ci zarafinsu, sannan a fitar da su gwargwadon niyyarsu
عربي Turanci urdu
Tsakanin ffsan fuka fukai arba'in, suka ce: Ya Abu Huraira kwana arba'in? Ya ce: Shin kun ƙi? Sai suka ce: Shekara arba'in? Ya ce: Na ki. Suka ce: Watan arba'in? Ya ce: Na ki
عربي Turanci urdu
«‌Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami*, idan yana da wani aiki na gari za'a ɗauka daga cikin shi gwargwadan zalincinsa, idan ba shi da wasu kyawawan ayyuka za'a ɗauka daga munanan ayyukan ɗan'uwansa (da ya zalinta) sai a jibga masa su».
عربي Turanci urdu
«‌Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya»*. Na ce: Ya Manzon Allah! mata da maza baki ɗaya sashinsu yana kallon sashi? Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «‌Ya A'isha, al'amarin ya fi tsanani a ce sashinsu yana kallon sashi».
عربي Turanci urdu
Mutane suna tsayuwa ne zuwa ga Ubangijin talikai har sai dayansu ya kasance ba ya cikin zabensa zuwa rabin kunnuwansa
عربي Turanci urdu
Lallai ne ku bada zuwa Ma'abotansa Ranar Al-kiyama har sai anyi sakamako ga Akuya Mai kaho da Mara Kaho
عربي Turanci urdu
Saihan da Jihan da Furat da Nil baki xayan su kogunan Al-janna ne
عربي Turanci urdu
Wuta da Aljanna sunyi Jayayya, sai wuta ta ce: an zaveni saboda masu girman kai, da Masu jiji da Kai, kuma Aljanna ta ce: Ni kuma babu mai shiga ta sai raunanan Mutane da waxanda ba komai ba, da wacanda idonsu bai buxe da Duniya ba
عربي Turanci urdu
Za'a tashi Mutane Ranar Al-qiyama -ko kuma ya ce Bayi= tsirara basu da Kaciya
عربي Turanci urdu
Lallai kafiri idan ya aikata Kyakkyawan aiki, sai a ciyar da shi Abinci a Duniya, Kuma Mumini Saboda Allah yana masa tanadin Kyawawan lada a Lahira, kuma ya bibiye shi da arziki a cikin Duniya kan biyayyarsa
عربي Turanci urdu
"Ladanai sune mafiya tsawon wuyaye a ranar alƙiyama".
عربي Turanci urdu
Haqiqa anyi mun Wahayi cewa ku za'a Jarrabeku a cikin Qabarinku kusan Fitinar Dujal
عربي Turanci urdu
Za a sami wani khalifa daga cikin magadanku a karshen zamani, yana rokon kudi ba ya kirgawa
عربي Turanci urdu
Idam Ranar Al-kiyama ta Kasance Allah ai Tura ga kowane Musuli Bayahude daya Ko banasare, sai yace wannan zai kwanceka daga Wuta
عربي Turanci urdu
Ku karanta Alqurani domin zai zo Ranar Alkiyama mai ceton Ma'abotansa
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
«Za'a kusantowa halitta da rana a yinin Alƙiyama har sai ta kusa kamar gwargwadan mil daga gare su»*, Sulaim ɗan Amir ya ce: Na rantse da Allah ban san me yake nufi da mil ba? Shin faɗin ƙasa ne, ko kuma mil ɗin da ake wa ido kwalli da shi? - ya ce: «Sai mutane su zama akan gwargwadan ayyukansu cikin gumi, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa idanun sawunsa, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa guwoyinsa, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa kwankwasonsa, daga cikinsu akwai wanda zai yi masa linzmi linzami» ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi nuni da hannunsa zuwa bakinsa.
عربي Turanci urdu
. :
عربي Turanci urdu
«Lallai mafi ƙankantar matsayin ɗayanku a cikin aljanna shi ne Ya ce masa: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, sai Ya ce da shi: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce da shi: @Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi».
عربي Turanci urdu
"Ni ne shugaban mutane a ranar alƙiyama, shin kun san daga menene hakan? @Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba*, sai mutane su ce: Shin bakwa ganin abinda haƙiƙa ya kai muku ? shin bakwa duba wanda zai yi muku ceto zuwa ga Ubangijinku ba? sai wasu daga mutane su ce wa wasu: Ku je gurin (annabi) Adam, sai su zo wa Adam - aminci ya tabbata agare shi - sai su ce masa: Kai ne uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya busa maka daga ranSa, kuma Ya umarci mala'iku sai suka yi maka sujjada, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana? sai Adam ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushi a yau bai taba irin wannan fushin ba, kuma ba zai taba yin irin wannan fushin ba, kuma lallai ni hakika Ya hanani daga bishiya sai na saba maSa, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Nuhu. Sai su zo wa (annabi) Nuhu sai su ce: kai Nuhu, lallai kai ne farkon manzanni zuwa mutanen kasa, hakika Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana, shin baka nema mana ceto ga Ubangijinka ba? sai ya ce: Lallai Ubangijina Ya yi fushi a yau bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba, kuma lallai cewa ni akwai mummunar addu'ar da na yi akan mutanena, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi gurin (annabi) Ibrahim. Sai su zo wa (annabi) Ibrahim sai su ce: kai Ibrahim, kai ne Annabin Allah kuma badaɗayinSa daga mutanen ƙasa, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce musu: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba irinsa, lallai cewa ni na yi ƙarya sau uku, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga (annabi) Musa. Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai Musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijnka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai ni naa kashe wani rai da ba'a yi umarni da in kasheta ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Isa. Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: kai Isa, kaine Manzon Allah kuma kalmarSa da ya jefata zuwa Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfidar goyo, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai Isa ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, ba zai anbaci wani zunubi ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -". Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce kai ne Manzon Allah kuma cika makin Annabawa, hakika Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai in tafi, sai in zo ƙarƙashin al’arshi sai infaɗi ina mai sujjada ga Ubangina, sannan Allah Ya buɗe mini daga godiyarSa da kyakkyawan yabo gareShi na wani abinda bai taɓa buɗewa wani a gabani na ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka shi, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in dago kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Uabngiji, sai ace: Ya Muhammad ka shigar daga al'ummarka wadanda babu wani hisabi akansu ta kofar dama daga kofofin aljanna, kuma su suna tarayya da mutane a koma bayan haka na kofofi". sannan ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lalai tsakanin ginshikai biyu daga ginshikan aljanna kamar tsakanin Makka ne da Hajar, ko tsakanin Makka ne da Busra".
عربي Turanci urdu
«Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske*, ba sa fitsari ba sa bahaya, ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abin taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski, kuma abin kunna tiraren wutarsu shi ne icen tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inun (Masu tsananin farin ido da tsananin ƙwayar baƙin da ke cikin idon), suna a kan halittar mutum ɗaya, akan surar babansu (Annabi) Adam, zira'i sittin a cikin sama».
عربي Turanci Indonisiyanci
«Akwai darajoji ɗari a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja kamar tsakanin sama da ƙasa ne, Firdausi it ce mafi ƙololuwarsu (a daraja), kuma daga nanne ƙoramun aljanna suke ɓuɓɓugowa, kuma a samanta ne Al’arshi yake. @Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi».
عربي Turanci Indonisiyanci