+ -

عن أسماء بنت أبي بكر رضي الله عنها قالت: قام رسول الله صلى الله عليه وسلم فَذَكَرَ الفتنةَ التي يُفتن بها المرء في قبره، فلما ذكر ذلك ضَجَّ المسلمون ضَجَّةً حالت بيني وبين أن أفهم كلامَ رسول الله صلى الله عليه وسلم ، فلما سَكَنَت ضَجَّتُهم قلتُ لرجل قريب مني: أيْ -بارك الله لك- ماذا قال رسول الله صلى الله عليه وسلم في آخر قوله؟ قال: «قد أُوحِيَ إليَّ أنكم تُفتَنون في القبور قريبًا من فتنة الدَّجَّال».
[صحيح] - [رواه البخاري مختصرا والنسائي]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Asma'a Bint Abubakar -Allah ya yarda da ita- ta ce: Manzon Allah SAW ya yi Wa'azin fitintinu waxanda Mutum zai gamu da su a cikin Qabarinsa, yayin da ya faxi haka sai Musulmai sai sukai kuwwa da ta hanani na fahimci abunda manzon Allah SAW yake nufi, yayin da kururuwar ta su ta ragu sai nace da wani Mutum da yake kusa da ni: Mai Manzon Allah yace Allah yayi maka Al-barka a qarshen maganarsa? sai ya ce: "Haqiqa anyi mun Wahayi cewa ku za'a Jarrabeku a cikin Qabarinku kusan Fitinar Dujal"
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi]

Bayani

Asma'u tana bada labarin cewa Manzon Allah SAW ya yi Wa'azin fitintinu waxanda Mutum zai gamu da su a cikin Qabarinsa,da tsoronsa, kuma ya faxi Fitinar Qabari, kuma abunda ake nufi da ita shi ne tamabayar Mala'iku biyu Munkarun da Nakiri, zasu tambayi bawa game da Ubangijinsa da Annabinsa da Addininsa, kuma ya faxi wannan fitina ce Maigirma, kuma duk wanda ya dace a wannan to ya rabauta, kuma duk wanda ya kasa to ya halaka, yayin da ya faxi haka sai Musulmai sai sukai kuwwa da ta hanani na fahimci abunda manzon Allah SAW yake nufi, yayin da kururuwar ta su ta ragu sai nace da wani Mutum da yake kusa da ni: Mai Manzon Allah yace Allah yayi maka Al-barka a qarshen maganarsa? sai ya ce: Haqiqa anyi mun Wahayi cewa ku za'a Jarrabeku a cikin Qabarinku kusan Fitinar Dujal, Saboda Fitinar Duja Mai tsanani ce kuma mai wuya haka ma Azabar Qabari.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa
Manufofin Fassarorin